An buɗe makarantu 45 da gwamnati ta rufe saboda barazanar tsaro, a Zamfara

0
561

Gwamnatin Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta sake buɗ makaranatu 45 cikin 75 da ta rufe a faɗin jihar saboda matsalar tsaro.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ambato Sakataren dindindin na ma’aikatar ilimi a jihar, Kabiru Attahiru na ya bayyana matakin lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin gaggawa kan ilimi a jihar a ofishinsa.

KU KUMA KARANTA: Tarihin Sinan al-Battani, mabuɗin ilmin Taurari

Attahiru ya ce gwamnati da jami’an tsaro na aiki tukuru domin tabbatar da cewa tsaro ya inganta a jihar.

”Muna sa ran kyautatuwar yanayin tsaro a Zamfara domin ganin mun bude sauran makarantu 30 da suka rage a rufe”, in ji Attahiru.

Gwamnatin Jihar Zamfara dai ta rufe makarantu a watan Satumban 2021 bayan garkuwa da daliɓan makarantar sakandaren Kaya da ke ƙaramar hukumar Maradun.

Leave a Reply