Gwamnatin Yobe Za Kafa Kamfanin Sarrafa Nama Don Haɓaka Kudaden Shigar Ta

0
621

Daga; Sani Gazas Chinade, Damaturu

GWAMNATIN Jihar Yobe tare da hadin gwiwar kamfanin kasar Masar, Messrs Los Amigos, sun kammala shirin kafa kamfanin sarrafa nama a Damaturu, babban birnin Jihar don haɓaka Kudaden Shigar ta. 

Kwamitin gudanarwa na jiha da hadin gwiwar kamfanin na Masar sun ziyarci Gwamna Mai Mala Buni, a wani bangare na matakan karfafa yarjejeniyar kafa kamfanin sarrafa naman. 

Kwamishinan kasuwanci na Jihar ta Yobe, Alhaji Barma Shettima ne ya jagoranci kwamitin gudanarwa na jiha, yayin da Injiniya Halal M. El-Ghor, ya jagoranci abokan hadin gwiwar kasar Masar wajen yiwa mai girma Gwamnan Jihar cikakken bayani kan aikin.

Tawagar ta yi wa Gwamna bayani kan manufar aikin, da yadda zai samar da kuɗaɗe ga gwamnati da yadda jadawalin aiwatar da shi zai kasance, tasirin sarkar darajar tattalin arziki da kuma inganta ingantaccen kiwo a Jihar.

Gwamna Buni ya bayyana kwarin guiwar cewa aikin zai haɓaka tattalin arzikin Jihar da al’ummar ta.

Ya yi nuni da cewa Jihar Yobe tana da dabarun kiwon dabbobi masu yawa don samar da nama mai inganci zuwa kasuwannin cikin gida da kuma fitar da su zuwa kasashen waje.

Buni ya bukaci ‘yan kwamitin da su mai da hankali tare da tabbatar da aiwatar da tsari mai kyau don yanayin ya kai ga nasara. 

A cikin kwamatin gudanarwa, akwai shugaban ma’aikata na gwamna, Alhaji Abdullahi Yusuf Gashua, babban sakataren gidan gwamnatin Jihar (PPS) Alhaji Liman Ibrahim, Dakta Idrissa Madaki da Alhaji Hamza Saidu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here