Kaduna 2023: Kanyip Ya Karyata Zancen Zaben Shi A Matsayin Abokin Takarar Uba Sani

0
284

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

MATAIMAKIN Shugaban Ma’aikata (Ofishin Mataimakin Gwamna), Jihar Kaduna, Barista James A. Kanyip ya bayyana an janyo hankalinsa bisa wani labarin da ke ta yawo a kafafen sada zumunta game da zaben sa a matsayin abokin takarar Sanata Uba Sani, dan takarar Gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Kaduna, inda ya ce ba gaskiya ba ne.

A wata sanarwa da mataimaki na musamman (kan kafofin yada labarai da sadarwa) na ofishin mataimakiyar gwamnan Jihar Kaduna, Peter Ibrahim ya sanyawa hannu a ranar Asabar, ya ce a sakamakon wannan jita-jita, an yi ta kiransa ta waya da tura masa sakonni.

Ya ce, ” don haka ina so na sanar da jama’a cewa mataimakin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati bai san cewa an tsayar da shi a matsayin mataimakin Sanata Uba Sani ba, don haka yana so ya raba kan sa da jita-jita da ke yaduwa.

Barista Kanyip ya ci gaba da cewa ya yi imanin cewa Sanata Uba Sani da jam’iyyar za su yi zaben su a lokacin da ya dace kuma su bayyana wanda aka zaba a bainar jama’a.

Ya godewa ‘ya’yan jam’iyyar bisa fatan alheri, amma ya shawarce su da su guji yada labaran da ba su da tushe da za su iya kawo cikas ga hadin kan jam’iyyar.

Leave a Reply