Gwamnatin Najeriya na duba yiwuwar soke kungiyar malaman jami’a ta ASUU

Wasu rahotanni sun bayyana da ke cewa gwamnatin Najeriya na duba yiwuwar soke ƙungiyar malaman jami’a ta ƙasar, wato ASUU idan ta ƙi janye yajin aikin da ta dade tana yi.


Gwamnatin ta kuma sanar da cewa ta amince a miƙa naira biliyan 100 ga ɓangaren ilimin jami’a ƙarƙashin wani yunƙurin da ta ke yi na warware matsalolin da suka janyo yajin aikin. baya ga wannan, gwamnatin ta kuma ware naira biliyan 50 ga ƙungiyoyin malaman jami’an a matsayin alwus-alawus domin su raba tsakanin rassan kungiyoyin.


Idan ba a manta ba, ASUU ta tsunduma cikin wannan yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairun wannan shekarar kuma ta ci gaba da sabunta shi zuwa wannan watan da muke ciki.


Majiyoyi daban-daban sun shaida wa jaridar Vanguard cewa ma’aikatar Ilimi ta kasar za ta iya soke kungiyar ta ASUU gaba dayanta idan kungiyar malaman ta ki nuna dattaku kan kokarin da gwmnatin Najeriyar ke yi kan warware wannan batun.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *