Gwamnan Kano ya biya wa ɗalibai 6,500 kuɗin JAMB ‘yan asalin jihar Kano

0
142

Daga Idris Umar, Zariya

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya biya wa Ɗalibai maza da mata, da suka gama sakandire ‘yan asalin jihar Kano kuɗin jarabawar share fagen shiga Jami’a kimanin 6,500 don ci gaba da karatun su a kwalejoji da jami’o’i a ƙasar nan dama duniya gaba ɗaya.

Gwamnan wanda ya fara da godiya ga iyayen yara bisa jajircewar su wajen bawa yaran su tarbiyya da tsayawa don ci gaban su ta hanyar ilimi.

Mai girma Gwamna yace daga lokacin da aka zaɓi wannan gwamnati sun gudanar da ayyuka da dama ya zuwa yanzu, inda ya ce lokacin yaƙin neman zaɓe sun yi wa al’umma da dama alƙawarin farfaɗo da harkar ilimi idan an samu nasara.

“Ba na mantawa wata shida da suka wuce mun ƙirƙiro da ɗaukar nauyin yaran mu da sukayi ƙwazo tare da ɗaukar su da biya masu kuɗin makaranta da sauran abubuwan da ba’a rasa ba.”

“Samun labarin wasu ɗaliban da muka tura ƙasashen ƙetare ba su samu kuɗin su ba ta fuskan matsalar canjin dala, ba mu yi ƙasa a gwuiwa ba ko bacci sai da muka tabbatar ya zuwa yanzu a sallame su babu mai bin wani abu.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kaduna zai ba da ilimi kyauta ga ɗaliban Kuriga

Gwamna Abba Kabir yace batun BESDA kuwa ya zuwa yanzu ya sa kwamiti da za su tantance su, wanda ya zuwa yanzu kuma an kammala tantance su, sai abin da ya yi saura.

”Kasancewar mun baiwa ilimi fifiko a jihar Kano ya sa wajen gabatar da kasafin kuɗin wannan shekara ya sa muka baiwa ilimi kaso mafi tsoka.”

Gwamnan ya kuma buƙaci Ɗalibai Maza da su ƙara ƙaimi wajen ganin sun samu dama kamar yadda mata suka yi ƙwazo don haka suma Maza ana buƙatar ƙara ƙaimin su.

Batun dawo da tsarin samar da kayan aiki kuwa gwamnan ya ba da umarnin ci gaba da samar da kayan aikin da suka haɗar da Tebura da kayan koyarwa da nan da bayan sallah za’a tabbatar da tura wa kowace makaranta a jihar Kano.

“Suma Malamai mun yi shirin ganin sun samu horo mai kyau tare da ba su haƙƙoƙinsu na alawus-alawus ɗin su da gwamnatin baya ba ta biya su ba.”

A jawabin sa mai girma kwamishinan ilimi na jihar Kano Hon Haruna Doguwa yace mai girma gwamna yana tuntuɓar sa a ko da yaushe yadda za’a tabbatar ɗaliban jihar Kano sun samu damar rubuta Jarabawar Jamb.

Doguwa ya kuma ce a lokuta da yawa yana mamakin yadda mai girma Gwamna ya ke fin sauran gwamnonin jihohin Najeriya ƙoƙari wajen gudanar da aiki tuƙuru.

Kwamishinan ya ce da irin aikin alherin da ya kema al’ummar jihar Kano zai ba shi damar yin aikin sa na tsawon shekaru takwas tare da wucewa mataki na gaba.

Sannan Haruna Umar Doguwa ya kuma ƙara da cewa a yanzu haka gwamnan Kano cikin ƙudurinsa na ciyar da ilimi gaba a kano ya ƙara wa ɗaliban makarantun kwana yawan harkar ciyarwa a faɗin jihar Kano.

Hajiya Rabi Inuwa Hussain wadda ta fara da godewa mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ƙoƙarin sa na tallafawa tsarin ilimi a wannan jiha don al’ummar sa su samu ilimi mai kyau.

Abba Kabir Yusuf ya kuma jinjina wa sauran ma’aikatan hukumar ilimi ta jihar Kano wajen ƙoƙarin da suka yi.

Bilala muhammad Abubuakr, Nahayatu Isah Garba, sun nuna godiyar su bisa yadda mai girma Gwamna ya taimaka Ɗaliban Kano 6,500 kuɗin Jarabawar JAMB da kowane Form ya kai Naira 6,200.

Ɗaya daga cikin iyayen yara Sada Muhammad Idris ya wakilci sauran iyayen yaran shi ma ya fara da godewa mai girma Gwamna bisa wannan ƙoƙari nasa.

Haka kuma yace a matsayin su na Iyayen yara za su ci gaba goyan baya ga duk wanda ke goyan bayan harkar ilmi a jihar Kano da yardar Allah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here