Gwamna Wike Ya Nemi Goyon Bayan Wakilan PDP Kaduna, Ya Bayar Da Tallafin Miliyan 200 Ga Yan Gudun Hijira

0
374

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

A CI gaba da rangadin neman kuri’u daga wakilan Jam’iyyar PDP a zaben fidda gwani na Jam’iyyar, Gwamna Nyeson Wike, a ranar Litinin ya kai ziyarar bazata Jihar Kaduna, inda a bayaninsa ya yi alkawarin korar jam’iyyar adawa ta All Progressives Congress (APC) daga Aso Rock idan har aka ba shi tikitin takarar shugaban kasa na Jam’iyyarsa.

Gwamnan Jihar Ribas ya sanar da bayar da gudunmawar naira miliyan 200 ga ‘yan gudun hijira da rikicin kabilanci ya shafa a Jihar ta Kaduna.

Wike ya samu rakiyar tsaffin gwamnonin Jihohin, Kaduna da Gombe, Ahmed Makarfi da Ibrahim Dankwambo zuwa sakatariyar Jam’iyyar inda shugaban Jam’iyyar PDP na jihar, Felix Hassan Hyat da sauran shugabannin Jam’iyyar suka tarbe shi.

Wike, ya caccaki gwamnati mai ci kan gazawa wajen sauke alkawurran da ta dauka a yakin neman zaben da ta yi wa ‘yan Najeriya, inda ya ce Jam’iyyar APC mai mulki ta sanya wa ‘yan Najeriya wahala a cikin halin kunci na tattalin arziki, rashin tsaro, hauhawar farashin kayayyaki, faduwar Naira da sauransu.

Ya ce “zaben 2023 zai zama muhimmin lokaci ga jam’iyyarsa don ta kawar da APC tare da samar da sabuwar alkibla ga kasar nan wajen farfado da tattalin arzikin kasar, inda ya bukaci wakilan Kaduna sama da 70 da su zabe shi a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben fidda gwani.

“Ina tabbatar muku, zan kayar da duk wani dan takarar APC a zaben 2023 mai gaskiya da adalci.

“Zan tsaya a kan kalamuna na sake gina wannan kasa da dora ta a kan turbar farfado da tattalin arzikin da aka kafa a kan tsaro, hadin kai, adalci da kuma sadaukar da rayuwar talakawa.

“Jam’iyyar mu tana bukatar mutum mai karfi da jajircewa wajen yin kokawar kwato mulki daga hannun APC kuma wannan mutumin shi ne Nyeson Wike,” ya tabbatar.

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP na riko, Ahmed Muhammad Makarfi ya bayyana cewa da ana bada mutum ne kawai a matsayin Shugaban kasa, to da ya nada Wike kai tsaye, domin a cewar sa dan Jihar ta Ribas ya mallaki duk wasu abubuwan da ake bukata na tsige APC, yana mai alkawarin ba da goyon bayansa da na wakilai ga mai neman takara.

Shugaban jam’iyyar PDP na Kaduna, Felix Hassan Hyat a nasa jawabin, ya yabawa Wike bisa tsayawa jam’iyyar a lokuta da dama a lokacin da ya fi dacewa, inda ya yi alkawarin yin amfani da kudaden da aka bayar don manufar da aka ba dasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here