Gobarar tankar mai ta ƙona gini 10 a jihar Ogun–NEMA

Rahotanni daga jihar Ogun a Kudancin Najeriya na cewa wata tanka maƙare da lita 45,000 na man fetur ta kama da wuta tare da sanadin lalacewar gine-gine 10 a yankin Ifo.

A cewar Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, lamarin ya faru ne da ƙarfe 7 na safiyar yau kan titin Olambe Matogun.

Gidan Talabijin na Channels ya rawaito Shugaban Hukumar NEMA, Mista Ibrahim Farinloye na cewa ba a samu asarar rayuka ba kuma babu wanda ya ji rauni sai dai gine-gine kimanin 10 sun rushe sakamakon ibtila’in.

Ya ce lamarin bai yi muni ba ganin yadda man ya riƙa bi ta hanyar ruwan da ke kusa da inda lamarin ya faru. A cewarsa, hakan ya kare al’ummar yankin daga shiga mummunan yanayi sakamakon haɗarin gobarar da ka iya shafar mutane da dama.

Tuni dai aka kashe wutar kamar yadda jami’in NEMA ɗin ya shaida.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *