Gobara a cibiyar sayar da gas a Kenya, ta kashe mutum 2 da jikkata fiye da 300

0
139

An samu gagarumar fashewar a wata cibiyar sayar da gas na girki a Nairobi, babban birnin Kenya inda aƙalla mutum biyu suka mutu kuma mutum 300 suka jikkata, kamar yadda ƙungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta Kenya da kuma jami’ai suka bayyana.

Lamarin ya faru ne ranar Alhamis da daddare, a cewar ganau. Ana fargabar cewa za a iya samun ƙarin mace-mace.

“Ma’aikatan bayar da agajin gaggawa daban-daban sun ƙuɓutar da mutum 271 inda aka kai su cibiyoyoin kiwon lafiya da ke Nairobi,” kamar yadda ƙungiyar ba da agaji ta Red Cross a Kenya ta bayyana ranar Juma’a a shafinta na X.

KU KUMA KARANTA: Tashin gobara a kasuwar waya a Damaturu, an yi asarar dukiya mai yawa

Ta ƙara da cewa an yi wa mutum 27 magani nan-take a wurin da lamarin ya faru.

Bidiyoyin da aka dauka a unguwar Embakasi sun nuna ‘yan kwana-kwana suna kokarin kashe gobarar.

Wani mai magana da yawun gwamnati ya bayyana cewa ana kokarin cika tukwanen iskar gas ne a lokacin da gobarar ta tashi da misalin karfe sha biyu na dare ranar Alhamis.

Ganau sun bayyana wa kafafen watsa labarai na kasar cewa sun ji mostin kasa bayan fashewar.

Leave a Reply