Connect with us

Raha

GAMON JINI: Wata Budurwa tayi iyo cikin ruwa daga Bangladesh zuwa Indiya don haduwa da masoyinta na Facebook

Published

on

Daga Fatima GIMBA, Abuja

ata budurwa ta kafa tahirin da ba a taba samu ba, inda ta tafi Indiya ta cikin ruwa tun daga kasar Bangladesh.

An bayyana matashiyar wacce tayi linkaya ( Iyo) ta ruwa zuwa kasar Indiya, tayi haka ne don zuwa ta gamu da saurayinta wanda suka hadu a kafar sadarwa ta Facebook.

Wannan shi ake kira soyayya gamon jini, isar budurwa keda wuya tayi gamo da saurayinta dan kasar Indiya, wanda suka hadu ta hanyar haduwar waya ko muce ta haduwar Facebook wanda wannan yasa ta yanke shawarar take har kasar Indiya domin ta aure shi.

Budurwa da aka bayyana sunanta, Krishna Mandal ta zabi ta ketara boda ta ruwa, a cewarta bata da passport wanda zata iya shiga cikin kasar Indiya ta kyakkyawar hanya.

Da ake zantawa da ita, Krishna tace tasha wahala a ruwan saboda sauran tsirrai da tarin abubuwan cikin ruwa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Ɗalibin jami’a ya rasu yana tsaka da rubuta jarrabawar ƙarshe a jami’ar Gombe

Published

on

Wani ɗalibin jami’ar jihar Gombe da ke zangon karatu na ƙarshe mai suna Abubakar Muhammad, ya rasu yayin da yake tsaka da rubuta jarrabawar kammala makarantar.

Ɗalibin dai na karatu ne a sashen koyon aikin Akanta na jami’ar.

Wani abokin karatun marigayin ya bayyanawa wakilinmu cewa marigayin ya zo ɗakin rubuta jarrabawa a ranar sai rashin lafiya ta kama shi inda nan take aka garzaya da shi zuwa cibiyar lafiya ta jami’ar dan duba lafiyarsa.

Sai dai a cewar majiyar, jikin ɗalibin ya tsananta, amma kafin nan rai ya yi halinsa, inda aka wuce da shi ɗakin adana gawarwaki a asibiti.

KU KUMA KARANTA: Amarya ta rasu ranar ɗaurin auren ta a Oyo

“Ya rasu a cibiyar lafiya ta jami’ar sannan daga bisani mataimakin shugaban sashen tsaro na jami’ar ya jagoranci ɗaukar gawar zuwa ɗakin adana gawarwaki na asibitin ƙwararru na Jihar Gombe tare da wasu abokansa da kuma wasu jami’an jami’ar,” in ji ɗalibin.

Da wakilinmu ya tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na jami’ar, Mohammed Abubakar, ya tabbatar da rasuwar ɗalibin.

Sai dai ya ce dama ɗalibin ba shi da lafiya a ranar tun kafin shigarsa ɗakin rubuta jarrabawar.

Continue Reading

Nishadi

Yadda Uba ya auri bazawara don nema wa ɗansa auren ‘yarta

Published

on

Wata bazawara ta kasance tana riƙon wata kyakkyawar budurwa. Duk wanda ya zo neman aurenta sai Bazawarar ta ce, ita ba za ta ba da aurenta ba sai an biya kuɗin aure da ɗawainiyarsa naira Miliyan 20, babu ragin ko sisi. Da yawan samari suka haƙura da aurenta.

READ ALSO: Almubazzaraci ya sa an kori ’yan sandan Imo bakwai, an gurfanar da su gaban kuliya

Wani saurayi, ya ga budurwar nan yana sonta, ita kuma ta gaya masa ƙa’idar aurenta. Saurayi ya je gida ya faɗawa Babansa tsarin auren budurwar da yake so. Saurayi ya ce, yana da Naira Miliyan 15 ta ribar kamfaninsa da ya samu.

Babansa ya ce, kawo miliyan 15 ɗin, saurayi ya kawo. Babansa ya ɗauke shi suka tafi gidan Bazawarar nan.

Babansa ya ce, zan yi magana amma kar ki katse ni sai na je ƙarshe. Bazawara ta ce, to.

Baban Saurayi ya ce, ga miliyan 5 kuɗin auren ‘yar da kike riƙo. Za ta yi magana ya ce, ta yi shiru. Ga kuma Naira miliyan 5, ni mahaifin wannan yaro na ganki ina sonki, zan aureki.

Take Bazawara ta ce masha Allah, Alhamdulillah! komai ya yi daidai, Allah ya bamu zaman lafiya. Sai a ɗaura kawai.

Mutane suka ce, ke da kike neman miliyan 20, ta yaya kika ƙare a miliyan 10? Sai ta ce Allah sarki, sayan jimla, ai ba daidai yake da sayan ɗaiɗai ba.

Shi kuma Saurayi ya yiwa babansa godiya ya ce, har canjin 5m na samu, sai a bani na ƙarasa ɗawainiyar biki. Baban ya ce, Kai ba ka da hankali ne, ba ka fahimtar lissafi, wannan miliyan 5 ɗin da ta rage mahaifiyarka za a bawa na dannar ƙirji.

Continue Reading

Allah Ɗaya Gari Bam Bam

Wasu ma’aurata sun biya ladan $1,000 ga wanda ya gano akunsu da ya ɓata

Published

on

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Rustoma babban Aku ne wanda ya tsere daga gidansu lokacin da aka bar ƙofa a buɗe.

Ɓacewar Rustoma ta shiga cikin kanun labarai, bayan da masu shi, wasu ƴan jihar Karnataka da ke kudancin Indiya suka sanya tukuicin kuɗi ga duk wanda zai iya dawo da shi.

Lokacin da aka dawo da Rustoma lafiya bayan kwana biyar, danginsa sun yi farin ciki sosai, har ma suka bayar da kyautar rufi 85,000, kwatankwacin naira 600,000, fiye ma da ladan da suka sanya tun da farko.

Lokacin da abokiyar zamansa Rio taga ya dawo gida bayan kwanaki biyar, ta yi farin ciki sosai har ta sumbace shi a baki.

Iyalan Shetty sun ce sun sayi akun biyu ne daga birnin Bangalore shekara uku da suka wuce.

Ba laifi ba ne kiwon aku a Indiya, amma masu ra’ayin kare haƙkin dabbobi na bayar da shawarar hana kiwo da cinikin tsuntsaye masu ban sha’awa a Indiya.

“A ko yaushe muna ɗaukar su a matsayin ɓangare na danginmu kuma ba mu taɓa yarda da saka su a keji ba,” in ji Arjun Shetty, wani ɗan kasuwa.

Tsuntsayen, in ji shi, suna son zama tare da iyalan, musamman Vihan, ɗan Mista Shetty me shekaru bakwai, kuma suna son kwaikwayon sautin da suke ji a kusa da su.

Rio (matar Akun) ta damu matuƙa da ɓacewar abokin zamanta har ta daina cin abinci.

Mista Shetty ya ce ya kashe maƙudan kuɗaɗe wajen bugawa da rarraba takardu masu ɗauke da hoton Rustoma, da kuma tukwicin da ya kai rufi 50,000.

Sun sanya allunan a kan tituna da dama a cikin garin Tumakuru, inda suke zaune. Iyalin kuma sun biya masu shela a unguwanni don zagayawa suna cigiyar Rustoma da lasifika.

Yayin da wannan ke faruwa, Rustoma bai yi wani nisa da su ba, don bai wuce kilomita uku da inda suke ba, inda ma’aikata biyu, Srinivas da Krishnamurthy ke kula da su.

Krishnamurthy ya samu Rustoma ne kwana guda bayan ya bar gida, inda ya ga tsuntsun zaune a saman bishiya, yana ƙoƙarin kare kansa daga maguna da karnuka, ya dube shi ya ga ya jigata ƙwarai saboda yunwa.

Rustoma ne ya amince ya tafi tare da Krishnamurthy, Bayan kwana huɗu a hannun mutanen sai mariƙansa suka ga cigiyar, nan take suka kira Shetty.

A lokacin ne suka gane cewa ladan ya ma fi abin da aka yi alkawari.

“Mun tuntuɓi wani limamin coci wanda ya ce Rustoma zai dawo nan da kwana uku, amma ya ce mana zai iya faruwa da wuri idan muka ƙara adadin ladan,” in ji Mista Shetty.

Lokacin da ya je karbar Rustoma, akun na zaune a cikin kejinsa, cikin tsananin bacin rai.

“Na so a ce kun ga yadda ya rikice lokacin da ya gan ni, nan da nan ya fara wasu surutai da yake yi duk sa’ad da yake cikin farin ciki da jin dadi”, in ji Mista Shetty, yana ƙyalƙyala dariya.

Duk danginmu sun yi murna da dawowar Rustoma, ba ma kamar Rio, Mista Shetty ya ce za su sanya ido ƙwarai ƙwarai a kan tsuntsayen a yanzu.

Sai dai girgizar da ɓacewar Rustoma ta haifar a danginsu, ta sa mutanen na tunanin ko tsuntsayen za su fi jin dadi a wani yanayi mai girma kamar gidan ajiye namun daji a Indiya ko kuma a waje.

“Shin iyaye ba sa tura ƴaƴansu ƙasashen waje don su yi karatu rayuwarsu ta yi kyau? Ai ba lallai ba ne su zauna tare da mu,” in ji shi.

“Idan za su fi farin ciki a can, a shirye muke mu amince da ra’ayinsu”.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like