Fursunoni 65, Ɗalibai 28,675 za su kammala karatunsu a Jami’ar NOUN

2
379

Mataimakin shugaban buɗaɗɗiyar jami’ar Nijeriya (NOUN), Farfesa Olufemi A. Peters, ya bayyana cewa ɗalibai 28,740 ne jami’ar zata yaye a taron da za a yi, kuma cikin su akwai fursunoni 65 daga gidan gyaran hali na Najeriya.

Farfesa Peters ya bayyana cewa 58 daga cikin fursunonin sun kammala karatun digiri ne, bakwai kuma sun kammala gaba da digiri ne, kuma suna karatu ba tare da tsada ba, domin jami’ar ta ba su tallafin karatu a matsayin wani ɓangare na al’amuran da suka shafi zamantakewa da kuma ba su damar cin gajiyar rayuwarsu bayan kammala wa’adinsu a gidan yari.

Da yake jawabi a taron share fage na jami’ar karo na 12 a ranar talata a Abuja, Farfesa Peters ya bayyana cewa yawan ɗaliban da suka kammala karatunsu na da yawa kuma shi ya sa aka kafa jami’ar domin samun damar ƙara wayar da kan al’ummar Najeriya da sauran damammaki.

KU KUMA KARANTA: Fursunoni ‘970 Suke Yin Digiri A Gidajen Yarin Najeriya’

Ya bayyana adadin ɗaliban da suka yaye sun haɗa da 21,339 waɗanda suka kammala karatun digiri 7,401 daga cikin waɗanda suka kammala karatun gaba da digiri 58 da kuma wadanda suka kammala karatun gaba da digiri 7 fursuna ne, inda ya ƙara da cewabɗalibai shida sun sami takardar digiri mai lamba ɗaya wato First Class, ɗalibai 2,306 sun sami takardun digiri masu daraja ta biyu na Upper sai 11, 075 da suka sami mataki na ƙarƙashin digiri mai lamba aji na biyu da kuma ɗalibai 5,558 da suka kammala karatu da digiri mai darajar aji na uku.

Yayin da ya bayyana cewa taron zai gudana ne a lokaci guda a cibiyoyin karatun jami’o’i 114 da ke fadin ƙasar nan domin samun ɗalibai da iyaye su sami shiga cibiyoyin da ke kusa da su, ya ce kusan ɗalibai 10,000 ne za su halarci bikin a Abuja wacce ta ƙunshi d
Ɗaliban da suka kammala karatu a cibiyar karatu ta Abuja da masu digiri na farko da duk waɗanda suka kammala karatu na gaba da digiri na farko (Postgraduate) da kuma dukkan ɗaliban da za su samu lambar yabo a fannonin karatunsu.

Da yake magana a kan batu ko kuma masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da ɗaliban da suka kammala karatun jami’ar ke fuskanta, ya ce ɗaliban nasu ba su son hakan. Ya ce wasu daga cikin dalilan na da nasaba da al’amuran da suka shafi kayan aiki, kuma jami’ar tana aiki da wata sabuwar shawara ga hukumar tare da fatan za ta ƙara shigo da wasu daga cikin ɗaliban zuwa hidimar ƙasa ta NYSC.

Mataimakin shugaban jami’ar ya kuma bayyana cewa jami’ar a kwanan baya ta samu cikakkiyar amincewar shirye-shirye guda 28 yayin da biyu kacal suka samu takardar shaidar wucin gadi, inda ya ƙara da cewa jami’ar tana da dalibai kusan 141,000 masu aiki da kuma kimanin 250,000 a lokacin da ake kara dalibai da waje.

A halin yanzu, ana sa ran Mataimakin Shugaban Jami’ar Afirka ta Kudu (UNISA), Farfesa Puleng Lenkabula zai gabatar da lacca mai taken “Volatility & Opportunities in Higher Education” a ranar Juma’a.

UNISA na ɗaya daga cikin tsofaffin jami’o’in koyon karatu daga nesa a Afirka kimanin shekaru 150 kuma Farfesa Lenkabula ita ce mace ta farko a matsayin mataimakiyar shugabar jami’ar wato VC.

2 COMMENTS

Leave a Reply