Fursunoni 11 a gidan yari na Kaduna sun kammala digiri

0
89
Fursunoni 11 a gidan yari na Kaduna sun kammala digiri

Fursunoni 11 a gidan yari na Kaduna sun kammala digiri

Fursunoni guda goma sha ɗaya daga gidan yari mai  matsakaicin tsaro a Kaduna sun sami digiri na farko da takardun shaidar babbar Difuloma  (PGD) daga Jami’ar NOUN.

Fursunoni bakwai sun kammala da kyakkyawan sakamako mai darajar Upper Second-Class, biyu sun samu Lower Second-Class, yayin da biyu suka sami takardun PGD. Waɗannan fursunoni sun kammala karatunsu ne ta hanyar cibiyar NOUN da ke gidan yari cikin shekaru huɗu zuwa biyar.

A lokacin wani ƙaramin bikin yaye fursunonin da aka yi a gidan yari na Kaduna, wakilin Mataimakin Shugaban Jami’ar, Dr. Baba, tare da Shugaban Kula da Gidajen Yari na Jihar Kaduna, Nuru Mohammed Isah, sun miƙa takardun ga fursunonin.

Dr. Baba ya yabawa jarumtar fursunonin wajen kammala karatunsu duk da ƙalubalen da suka fuskanta a matsayin waɗanda aka kulle.

Shugaba Isah ya kuma jinjinawa fursunonin bisa ƙoƙarinsu na cimma nasara a fannin karatu duk da ƙalubalen zamantakewa da ke tattare da karatu a gidan yari.

Haka nan, Mataimakin shugaban masu kula da Gidajen Yari, Abdullahi Dangani, ya gode wa NOUN bisa gudunmuwar da ta bayar wajen kyautata halayen fursunonin.

Leave a Reply