Aƙalla manoma 500 ne suka ci gajiyar aikin noma da Gwamnatin jihar Yobe ta raba wa al’ummar Jare ranar Lahadi.
Gwamnatin jihar ta bayyana rabon kayayyakin a matsayin wani ɓangare na shirin farfaɗo da jihar tun da wuri.
Da yake ƙaddamar da rabon kayayyakin a ranar Lahadi, Dokta Mohammed Goje, Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), ya bayyana cewa kowanne daga cikin waɗanda suka amfana zai koma gida da buhuhunan ajiye kayan gona, abin feshi, takin ruwa, maganin ciyawa, irin wake, dawa, safar hannu, da abin rufe fuska.
Rahotanni sun bayyana cewa shirin bunƙasa noma (ADP) ne ya zaɓo waɗanda suka ci gajiyar 500 ta hanyar zaɓin al’umma. An tattaro cewa waɗanda suka amfana 500 sun haɗa da maza 400 manoma da mata 100 manoma na al’ummar.
Daga bisani, waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun yabawa gwamnatin jihar kan yadda ta zaɓo al’ummarsu ta Jajere a cikin al’ummomin da suka amfana.