El-Rufa’i: Mun Gaza A Matsayinmu Na Shugabanni A Najeriya

2
414

Daga; Rabo Haladu, Kaduna.

GWAMNAN Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya nemi gafara al’umma bisa hare-haren da ‘yan bindiga da ke ci gaba da salwantar da rayukan a yankunan Jihar Kaduna, musamman harin da aka kai wa jirgin kasa a ranar Litinin.

Gwamnan, wanda cikin yanayi mai cike da damuwa ya ce haƙiƙanin gaskiya yana cikin matuƙar bakin ciki saboda rabonsa da ya yi bacci tun ranar litinin kuma ba ya iya bacci ko da ya sha maganin bacci saboda tsananin tashin hankali.

El-Rufa’i ya yi waɗannan kalamai ne lokacin da ya je karamar hukumar Giwa domin bai wa al’umma hakuri da ta’azziya da jaje bisa abubuwan da ke faruwa.

Ya kai ziyarar ne a ranar Alhamis ƙarƙashin rakiyar mataimakiyarsa Hajiya Hadiza Sabuwa Balarabe da kuma wasu mukaraɓan gwamnatinsa.

wani saƙon murya da masu taimaka wa gwamnan kan yaɗa labarai suka bayana cewa gwamnan ya ce hakkin shugabanci abu ne da wata rana zai tashi ya tsaya gaban Ubangiji domin ya yi bayyani kan abubuwan da ke faruwa da abubuwan da ya aiwatar.

“Hakkin shugabanci kamar yadda malamai da jagoran addinin kirista suka fada, abu ne wanda wata rana zan tsaya gaban Allah SWT in yi bayanin me na yi don tabbatar waɗannan abubuwa ba su faru ba.

“Ina tsoron wannan rana da zan tsaya a gaban Allah na fadi me na yi, me zan iya cewa mun yi? Saboda haka dole mu roƙi gafararku da afuwarku domin a gwamnatance mu muka kasa.

“Kuma al’umma da laifinku, amma zan zo kanku tukunna,” in ji shi’

Nasir El-Rufa’i ya ce babu shaka sun gaza a gwamnatance kuma ba su da wata hujja domin koma me ke faruwa ba su da bakin magana domin hakki ne da ya rataya a wuyansu su tashi tsaye su kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Gwamnan ya ce yana tsoron ranar gamuwarsa da Allah domin bayyani kan abubuwan da ya yi me zai iya cewa?

Sai dai ya ce su ma al’umma da nasu laifin amma sai dai kowane irin laifi suka yi hakki na gwamnati ne kuma laifi nasu ne.

“Ni a ganina wadannan matsaloli ba su da wahala amma a yanzu sun kasance masu wahala, shekara biyu zuwa uku da suka wuce, mun san inda ‘yan ta’addan nan suke, mun san komai, akwai jiragen sama da ke ba mu bayanai da sojoji da ‘yan sanda da jami’an tsaro na SSS.

“Ko waɗannan masu aikata wannan ta’addanci an san da su domin an kashe wasu a cikinsu a baya.

Gwamna Elrufai ya ce ganin tashin hankali da ƙaruwar hare-haren nan akwai lokacin da ya ba da shawarar cewa a shiga dazuzzuka da suka kasance maboyar wadannan ‘yan ta’adda a ƙona su da kauyuka da dazukan baki daya.

Amma a cewar gwamnan bai samu goyon-baya ba saboda sojoji na cewa ai tun da ba yaƙi ake yi ba, idan har suka aikata hakan to nan gaba suna iya fuskatar matsala.

Gwamnan ya ce sojoji sun ba da hujjar cewa su tsoronsu shi ne nan gaba ana iya kama su idan suka bar aiki suka fita ƙetare a gurfanar da su kan laifin aikata laifukan yaƙi ko kashe fararen-hula.

nuna takaicinsa kan yadda masu kashe waɗannan mutanen ba a ganin laifinsu, dai dai ya ce tun lokacin da kotu ta amince a ayyanasu a matsayin ‘yan ta’adda suke ta matsa ƙaimi kan a ƙona dazukan, amma an ƙi sauraronsu.

2 COMMENTS

Leave a Reply