Dubun wata mace da ta ƙware a garkuwa yara ta cika

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wata mata mai shekaru 27 mai suna Maryam Ayila, da ake zargi da laifin yin garkuwa da wata yarinya ‘yar shekara 13, mai suna Sofiat Yusau.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, SP Abimbola Oyeyemi ya sanyawa hannu, ya ce an kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da wani Ismail Yusau ya kai wa ‘yan sandan da ke aiki a Agbara, inda ya bayyana cewa, ya aiki ‘yarsa kasuwar Agbara ne, kawai sai ya ga kira ta wayar salula a wani baƙuwar lamba, sa’o’i kaɗan da aken ‘yar tasa, inda aka sanar da shi ta wayar cewa an sace ‘yarsa, kuma idan har bai aika da kuɗi naira dubu 250,000 a matsayin kuɗin fansa ba, ba zai sake ganin ‘yar sa ba.

KU KUMA KARANTA:‘Yan sandan Gombe sun kama wasu matasa 4 bisa zargin yin garkuwa

“Bayan rahoton, DPO na Agbara, CSP Abiodun Salau, ya tattara ‘yan sanda masu binciken na rundunar Crack Detectives, waɗanda suka fara gudanar da bincike na fasaha da leken asiri.

“Kokarin da suka yi ya haifar da sakamako mai kyau, a lokacin da aka gano wanda ake zargin a maɓoyar ta a unguwar Atan a Ota, inda nan take aka kama ta, aka kuma ceto yarinyar ba tare da wani rauni ba.

“Bincike na farko ya nuna cewa wanda ake zargin ta yi garkuwa da wata yarinya a unguwar Itele Ota a ranar 19 ga watan Disamba, 2022, kuma an biya ta kuɗin fansa kafin ta sako wanda ta kama,” in ji shi.

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sanda, CP Lanre Bankole, ya bayar da umarnin miƙa wanda ake zargin ga sashin yaƙi da garkuwa da mutane na sashen binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi gaban kuliya.


Comments

3 responses to “Dubun wata mace da ta ƙware a garkuwa yara ta cika”

  1. […] KU KUMA KARANTA:Dubun wata mace da ta ƙware a garkuwa yara ta cika […]

  2. […] KU KUMA KARANTA:Dubun wata mace da ta ƙware a garkuwa yara ta cika […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *