Connect with us

Jan hankali

Dalilai 7 masu Haɗari da zai sa mu guji cin gandar fatar dabbobi

Published

on

Itadai ganda farin jini gareta, musamman idan tayi laushi. Kusan kowanne ƙabila a Najeriya suna so kuma suna cin gandar. Yarabawa na kiransa ‘Ponmo’, Inyamurai kuma ‘Kanda’, Hausawa kuwa na cewa ‘Ganda’, fatar dabbobi na daga cikin abincin da ‘yan Najeriya ke ci ba kakkautawa.

Gwamnati ta ce sam bai kamata jama’a suke cin wannan nau’in naman ba saboda yana rusa masana’antun fatu a kasar. A 2019, hukumar kula da abinci da magunguna NAFDAC ta gargadi ‘yan Najeriya game da cin ganda, inda tace yana da matsala ga lafiya.

Daraktan NAFDAC, Moji Adeyeye ya ce, bincike ya nuna ‘yan kasuwa na siyar da fatun da ya kamata ace na masana’antu ne zuwa abincin da ake ci.

Duk da gargadin illa ga lafiya da kuma durkusar da masanatun fata, har yanzu ganda na daga cikin abincin ‘yan Najeriya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ga jerin illolin cin ganda

Da yawan fatun dabbobi ana samar dasu ne don amfanuwar masana’atun fatu, amma ake samunsu a tukwanen jama’a. Don haka, akwai illa ga lafiyar dan adam a cinsa.

Wasu daga cikin fatun da ake kawo wa kasuwa suna dauke da sinadaran ajiya masu illa, wadanda ka iya cutar da jikin dan adam.

Wasu fatun da ake kawowa daga ƙasashen waje ba na ci bane, ana kawowa ne domin aiki dasu a masarrafar takalma da jaka da sauransu, ba shakka hakan matsala ne ga lafiya.

Fatun da ake kawowa daga kasashen waje sun fi araha saboda illarsu, kuma basu da tsaftar da fatun da ake samu a gida Najeriya. Wannan yasa ‘yan kasuwa ke kawowa don riba, ‘yan Najeriya kuwa ke ci cikin rashin sani duk da illolinsa.

Ya kamata masu kiwon dabbobi su sani cewa, fatun da ake kawowa don masana’antu ba na amfani bane a sarrafa abincin dabbobi. Amfani dasu kuwa matsala ce ga lafiyar jama’a.

Akwai yiwuwar samun matsalar hanta, koda da bugun zuciya ta dalilin ganda, ga kuma wasu karin cututtuka dake tattare da cinsa.

Yadda ake sarrafa fatu na daya daga cikin hanyoyi mara natuswa, don haka akwai yiwuwar samun barazanar lafiya daga cin irin wadannan fatun.

2 Comments

2 Comments

  1. Pingback: Dalilai 7 masu Haɗari da zai sa mu guji cin gandar fatar dabbobi – LEGEND FM DAURA

  2. Pingback: Yadda miji ya guji matarsa saboda gemu ya fito a fuskarta | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

CBN

Jabun kuɗaɗe sun bazu a gari — CBN

Published

on

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ja hankalin ’yan Najeriya kan jabun takardun kuɗin ƙasar da ke yawo a cikin al’umma a sakamakon raɗe-raɗin da ake yaɗawa na ƙarancin tsabar kuɗi.

Kakakin CBN, Hakama Sidi Ali ta shawarci al’umma da su kasance masu lura ganin cewa masu jabun kuɗaɗe na amfani da su a matsayin kuɗin mota ko a wurin yin cefane da gidajen abinci sauransu.

Sanarwar ta CBN ta ce “Dokar CBN ta tanadi hukucin ɗaurin aƙalla shekaru biyar ga duk wanda ya buga jabun kuɗaɗe.

“CBN na aiki da hukumomin tsaro da na hada-hadar kuɗaɗe wajen ganowa da ƙwace jabun kuɗaɗe da kuma tsare masu buga su.” in ji jami’ar.

Daga nan sai ta umarci bankuna, ’yan canji da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe da su ɗauki matakan da suka dace wajen ganowa da kuma hana yaɗuwar jabun kuɗaɗe.

Ta ƙara da cewa, “ana ƙira ga jama’a su kai ƙarar duk wanda suka ga yana yin jabun kuɗaɗe ga ofishin yan sanda ko na CBN mafi kusa.

Continue Reading

EFCC

EFCC ta fitar da matakai takwas na kare kai daga masu damfara da katin ATM

Published

on

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zangon ƙasa a Nijeriya, EFCC ta koka kan yadda take yawan samun rahotanni na waɗanda aka cire wa kuɗi daga banki ba tare da saninsu ba kuma akasari ta ATM.

Hukumar ta ce akasarin ƴan damfarar sun fi samun bayanan jama’a ko katin ATM ɗin mutane a wuraren cirar kuɗi na ATM ko kuma masu POS.

EFCC ta yi gargaɗi kan cewa ƴan damfarar suna amfani da katin ATM na bankin mutumin da suke so su yaudara, bayan haka sukan je wurinsa da niyyar taimako idan ya shiga ruɗani a gaban ATM.

Hukumar ta ce ƴan damfarar kan yi sauri su yi wa kwastoman bankin musaya da katinsa bayan su haddace lambobin sirrinsa a lokacin da suke ƙoƙarin taimakonsa, wanda daga baya sai su cire kuɗin da ke asusun ajiyarsa.

Dangane da haka ne hukumar ta fitar da hanyoyi takwas waɗanda take ganin idan jama’a sun bi su za su samu kariya daga masu damfarar:

KU KUMA KARANTA: EFCC za ta gurfanar da sojojin saman Najeriya a kotu kan zargin damfara a intanet

  1. Akwai buƙatar ajiye kati a aminctaccen wuri. Duk lokacin da ka karɓi katinka bayan cire kuɗi, ka tabbata katinka ka karɓa ba wai wanda ke kama da katinka ba.
  2. A rinƙa duba sauran kuɗin da ke asusu (balance) domin dubawa ko an cire kuɗi daga asusu.
  3. Saka ƙararrawa domin lura da duk wani abu da ya shafi asusun ajiya ko katin banki.
  4. Rufe lambobin da ake latsawa a jikin ATM ko POS da hannu a lokacin da ake saka lamobin sirri domin cire kuɗi ko wani amfani.
  5. A rinƙa neman taimako daga jami’an banki, ka da ka yi saurin biyan kuɗi ko cire kuɗi.
  6. A ƙira banki domin toshe katin ATM a duk lokacin da aka lura kati ya maƙale a cikin ATM ko kuma duk lokacin da aka lura da wani lamari wanda yake ba daidai ba.
  7. A tabbata an san lambar da za a iya toshe ATM da ita tare da amfani da ita cikin gaggawa a duk lokacin da aka ɓatar da katin ko aka sace shi.
  8. A latsa lambobin USSD na 966911# da kuma bin matakan da suka biyo baya domin toshe katin ATM nan take.
Continue Reading

Jan hankali

NUJ jihar Yobe, ta nuna rashin jin daɗi da ƙara farashi da masu gidajen mai suka yi

Published

on

Daga Ibraheem EL-TAFSEER

Ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Yobe ta bayyana rashin jin daɗin ta game da halin rashin kishin ƙasa da wasu masu gidajen man fetur da ma’aikata suka yi a Damaturu, babban birnin jihar Yobe da sauran ƙananan hukumomin jihar, dangane da ƙarancin man fetur da aka samu a yau da kuma ƙaruwar farashin mai ɗin, wanda hakan ya jawo dogon layi a gidajen man.

A wata takarda da ƙungiyar ta fitar, wanda shugaban ƙungiyar ‘yan jarida na jihar Yobe, Kwamared Rajab Mohammed da sakatatensa Alhassan Sule Mamudo suka sa wa hanu, ta bayyana cewa, ƙungiyar ta damu matuƙa da halin da ‘yan jihar ke ciki masu son zaman lafiya.

KU KUMA KARANTA: Cire tallafin man fetur ya jawo hauhawar farashin mai a Najeriya

Don haka muna ƙira ga hukumomin tsaro, hukumomin gwamnati, hukumomin da abin ya shafa da duk masu ruwa da tsaki da su gaggauta ɗaukar matakan da suka dace don ganin an kawo karshen wannan mummunan yanayi da ke iya lalata tattalin arziƙin al’umma.

Za mu iya kwatanta shi a matsayin zagon ƙasa ga tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya. Ƙungiyar za ta ci gaba da sanya ido kan lamarin tare da sanar da ‘yan ƙasar kan duk wani ci gaba mai kyau tare da yin ƙira ga kowa da kowa da su kwantar da hankula domin za a shawo kan lamarin cikin ruwan sanyi.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like