Dalilai 7 masu Haɗari da zai sa mu guji cin gandar fatar dabbobi

2
760

Itadai ganda farin jini gareta, musamman idan tayi laushi. Kusan kowanne ƙabila a Najeriya suna so kuma suna cin gandar. Yarabawa na kiransa ‘Ponmo’, Inyamurai kuma ‘Kanda’, Hausawa kuwa na cewa ‘Ganda’, fatar dabbobi na daga cikin abincin da ‘yan Najeriya ke ci ba kakkautawa.

Gwamnati ta ce sam bai kamata jama’a suke cin wannan nau’in naman ba saboda yana rusa masana’antun fatu a kasar. A 2019, hukumar kula da abinci da magunguna NAFDAC ta gargadi ‘yan Najeriya game da cin ganda, inda tace yana da matsala ga lafiya.

Daraktan NAFDAC, Moji Adeyeye ya ce, bincike ya nuna ‘yan kasuwa na siyar da fatun da ya kamata ace na masana’antu ne zuwa abincin da ake ci.

Duk da gargadin illa ga lafiya da kuma durkusar da masanatun fata, har yanzu ganda na daga cikin abincin ‘yan Najeriya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ga jerin illolin cin ganda

Da yawan fatun dabbobi ana samar dasu ne don amfanuwar masana’atun fatu, amma ake samunsu a tukwanen jama’a. Don haka, akwai illa ga lafiyar dan adam a cinsa.

Wasu daga cikin fatun da ake kawo wa kasuwa suna dauke da sinadaran ajiya masu illa, wadanda ka iya cutar da jikin dan adam.

Wasu fatun da ake kawowa daga ƙasashen waje ba na ci bane, ana kawowa ne domin aiki dasu a masarrafar takalma da jaka da sauransu, ba shakka hakan matsala ne ga lafiya.

Fatun da ake kawowa daga kasashen waje sun fi araha saboda illarsu, kuma basu da tsaftar da fatun da ake samu a gida Najeriya. Wannan yasa ‘yan kasuwa ke kawowa don riba, ‘yan Najeriya kuwa ke ci cikin rashin sani duk da illolinsa.

Ya kamata masu kiwon dabbobi su sani cewa, fatun da ake kawowa don masana’antu ba na amfani bane a sarrafa abincin dabbobi. Amfani dasu kuwa matsala ce ga lafiyar jama’a.

Akwai yiwuwar samun matsalar hanta, koda da bugun zuciya ta dalilin ganda, ga kuma wasu karin cututtuka dake tattare da cinsa.

Yadda ake sarrafa fatu na daya daga cikin hanyoyi mara natuswa, don haka akwai yiwuwar samun barazanar lafiya daga cin irin wadannan fatun.

2 COMMENTS

Leave a Reply