Daga Ibraheem El-Tafseer
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta gurfanar da waɗanda suka kashe marigayi wakilin Muryar Najeriya (VON) Hamisu Ɗanjibga.
Idan za a iya tunawa a kwanakin baya aka kashe wani Hamisu Ɗanjibga a gidansa makonni uku da suka wuce kuma an jefa gawar tasa a wani rami na bahaya a bayan gidansa.
Da yake gabatar da waɗanda ake zargin su biyu, kwamishinan ‘yan sandan CP Shehu Mohammed Dalijan ya ce ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, ɗan’uwan marigayi Hamisu Ɗanjibga ne mai suna Mansur Haruna.
A cewar kwamishinan, Haruna wanda ke zama a gidan marigayi Ɗanjibga ya bayyana cewa shi ne ya gayyaci abokinsa Ibrahim Na Baba domin ya taimaka masa ya kashe kawunsa marigayi Ɗanjibga saboda shi marigayi Ɗanjibga bai taimaka masa ya shiga aikin sojan Najeriya ba ko aikin Ɗan sanda.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda a Zamfara sun kama waɗanda ake zargi da kisan ɗan jarida a jihar
Kwamishinan ya ce, “Mansur Haruna ya amsa cewa shi ne ya gayyaci abokinsa Ibrahim Na Baba domin ya taimaka masa ya kashe kawunsa marigayi Ɗanjibga”.
“Mansur Haruna ya ce ya zauna a gidan marigayi Ɗanjibga sama da shekaru 17 kuma yana son shiga sojan ko kuma aikin ɗan sanda, amma marigayi Ɗanjibga ya ce ba zai goyi bayan burinsa ba saboda munanan halayensa.” In ji shi
Ya ce ”Danjibga a ƙarshe ya kore shi daga gidansa saboda ya ƙi canza ɗabi’arsa.” Mansur bai ji daɗin hakan ba, ya amsa cewa ya gayyaci abokinsa ne domin ya taimaka masa wajen sace kawun nasa marigayi Ɗanjibga domin ya samu kuɗi ya fara kasuwanci”.
Da yake zantawa da manema labarai, wanda ake zargin Mansur Haruna ya ce a lokacin da suka shiga ɗakin marigayi Hamisu Ɗanjibga, sun yi iƙirarin cewa su ‘yan bindiga ne, suka ce ya bi su dajin amma ya ƙi zuwa.
Ana cikin yin garkuwa da shi sai rigar da Mansur Haruna ya rufe fuskarsa ta faɗi, nan take marigayi Ɗanjibga ya gane shi, don haka suka yanke shawarar kashe shi.
Ya ce, “Lokacin da muke ta faman fitar da shi daga ɗakinsa, abin rufe fuskana ya faɗi, da sauri ya gane ni ya ce’ “Mansur, me kake yi a nan?”.
“Da sanin cewa ya gane ni, sai na kawo wuƙa na daɓa masa sau biyu ya riƙe ni sosai” sai “Abokina Ibrahim Na Baba shi ma ya fito da adda ya sareshi shi a kai inda daga bisani ya faɗi ya mutu nan take”.
“Mun ɗauki gawarsa da sauri muka jefar da ita a wani rami na kashi a bayan gidansa muka sanya siminti muka rufe bakin”. inji shi.