Daga IMRANA ABDULLAHI Kaduna
Gwamnan Jihar Zamfara Dokta Bello Muhammad Matawalle ya bayyana cewa babban kalubalen da ke gaban duk wani ma’aikacin Gwamnatin Jihar Shi ne yin aiki tukuru bisa tsarin bin doka da ka’ida domin ciyar da Jihar gaba.
Gwamna Muhammad Bello Matawalle ya tabbatar da cewa kalubalen da ke gabansa shi ne ya samu cika burinsa na samar da Samuwar Jihar Zamfara da kowa zai yi alfahari da ita.
Gwamnan ya yi kira ga daukacin ma’aikatan Jihar da su kara rubanya kwazon aiki wajen ganin an gina sabuwar Jihar Zamfara mai inganci da yaya, Jikoki za su yi tunkaho da ita.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen taron bude samar da horaswa na kwanaki biyar ga jami’an Gwamnatin Jihar da aka yi a garin Abuja.
Taron mai taken samar da kyakkyawan shugabanci domin ci gaba an shirya shi ne tsakanin Gwamnatin Jihar tare da hadin Gwiwar wata makarantar Koyar da dabarun kasuwanci da le Ibadan.
Gwamna Matawalle ya ci gaba da bayanin cewa “ina kara jadda kira a gare ku da ku kara zage damtse wajen dadewa domin mu kawar da matsalar yan bindiga da nufin samar da Jiha ingantacciya da ke kan hanya dai dai da kowace Jiha ta hanyar aikinta arzikin da Allah ya ba mu a cikin Jihar.
Gwamnan ya lissafa wa mahalarta taron wadansu muhimman al’amuran da Gwamnatinsa Gwamnatinsa Sanya a gaba da nufin tsare gaskiya da adalci wajen tafiyar da aikin Gwamnati.
“Ina murna da farin cikin shaidawa duniya cewa dokar hana bautar da kananan yara da kuma ta kara inganta rayuwar masu bukata ta musamman da zarar an kawo ta gabana San Sanya wa dokar hannu”, Inji Gwamna Matawalle.
Kafin in kammala jawabi na ina son yin amfani da wannan dama in bayyana farin ciki da murna ga shugabar ma’aikatan Gwamnatin tarayya uwargida Folashade Mejabi Yemi – Esan, bisa kokarin da ta yi na halartar wannan taro duk da irin dimbin ayyukan da ke gabanta amma ta halarci wannan taron da kanta.
“Hakika wannan babban taro ya zo a lokacin da ya dace saboda Jihar Zamfara na matukar bukatar kwararru kuma hazikan mutanen da za su gudanar da aikin ci gaban Jihar.
An dai shirya taron ne ga kwamishinoni,Masu bayar da shawara,da kuma jami’an Gwamnatin Jihar Zamfara a ranar 17 ga watan Janairu 2022 a otal din rock view da ke Abuja.