Buhari ya yi tir da kashe basarake tareda mutanen ƙauye a Jihar Imo

0
514

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya ba da umarnin gudanar da bincike kan kisan da aka yi wa Eze Asor, basaraken al’ummar Obudi-Agwa, da wasu mutum huɗu wadanda aka kashe mutanen ƙauyen, waɗanda suka rasa rayukansu a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari fadar sarkin da ke ƙaramar hukumar Oguta a jihar Imo.

Shugaba Buhari, a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Garba Shehu, ya fitar a ranar Talata ya yi tir da Allah wadai da harin tare da jajantawa iyalan waɗanda suka rasu.

Sanarwar ta ce, Shugaban ya umurci hukumomin tsaro a jihar da su tsananta bincike kan wannan aika-aika tare da tabbatar da cewa waɗanda suka yi aikata-aikar sun fuskanci fushin doka.

Yayin da yake jajantawa ‘yan uwa, abokan arziki, al’ummar Obudi-Agwa, da kuma duk waɗanda harin ya shafa, shugaban ya yi addu’ar Allah ya bai wa waɗanda suka jikkata sauƙi cikin gaggawa.

Shugaba Buhari ya yaba da irin ƙoƙarin da gwamnatin jihar Imo ke yi na inganta harkar tsaro, ya kuma ƙarfafa gwiwar ɗaukacin al’ummar Imo da ‘yan ƙasa da su bayar da goyon baya ga ƙoƙarin haɗin gwiwa na ‘yan jihar da sauran al’ummar yankin domin kiyaye kowa da kowa.”

A halin da ake ciki, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Imo, CSP Michael Abattam, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce nan take rundunar ta samu kiran gaggawa cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin mambobin haramtacciyar Ƙungiyar Biafra ne da kuma ƙungiyar ‘yan ta’addan ta, Eastern Security Network, sun far wa fadar basaraken.

Ya ce, Jami’in ‘yan sandan shiyya, tare da tawagar ‘yan sandan rundunar, nan take suka garzaya zuwa fadar, inda suka isa, aka gano cewa ‘yan bindigar sun gudu daga wurin.

“Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa ɓarayin sun zo ne a cikin motoci huɗu da babura biyu tare da wata mata inda suka yi kama da wadanda ke cikin halin kunci da suka zo suka kai masa rahoton wani lamari na gaggawa.

“Sarkin da bai yi tsammanin miyagu ba ne, sai ya ba su izinin shiga fadarsa, ya zauna da su, suna cikin bayyana dalilin ziyarar nasu, sai suka fito da bindigogi, suka harbe sarkin da mukarrabansa biyu, sannan suka yi gaggawar ficewa daga fadar.

“A kan hanyarsu ta zuwa ne suka kai hari ofishin ‘yan banga na Agwa, suka harbe mutum daya sannan suka tafi da babura uku.

“Jami’an ‘yan sanda ɗauke da bayanai daga shaidun gani da ido, sun bi hanyar da ‘yan bindigar suka tsere ne domin nemansu” inji shi.

Abattam ya ce an ajiye gawarwakin mamatan a ɗakin ajiyar gawarwaki, inda ya ƙara da cewa an yi wa al’ummar garin kariya da isassun jami’an ‘yan sanda.

Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mohammed Barde, wanda ya yi Allah wadai da wannan danyen aikin, ya yi kira da a kwantar da hankula, inda ya ce rundunar ba za ta bar wani abu ba har sai an kama wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da fuskantar fushin doka akan su.

Leave a Reply