Buhari Ya Tafi Taron AU Da AU A Kasar Beljiyom

0
414

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na kan hanyar zuwa halartar taron kungiyar Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka karo na 6 a birnin Brussels na kasar Belgium.

Mahalarta taron da zai gudana tsakanin 17 – 18 ga Fabrairu, 2022, za su tattauna kan batutuwan da suka shafi duniya a halin yanzu.

Irin waɗannan wuraren tattaunawa sun haɗa da: Ba da Kuɗaɗe don Ci gaba mai ɗorewa; Canjin yanayi da Canjin Makamashi, Yanar gizo da Sufuri, Zaman Lafiya, Tsaro da Mulki; da Tallafin Sana’o’i masu zaman kansu da Haɗin Tattalin Arziƙi.

Buhari ya yi bulaguro
Buhari ya yi bulaguro

Sauran sun hada da: Ilimi, Al’adu da Koyarwar Sana’o’i, Hijira; Noma da Ci gaba mai dorewa da Tsarin Lafiya da Samar da rigakafin.

Tawagar ‘yan rakiyar Shugaban sun hada da Ministan Harkokin Waje, Ambasada Geoffrey Onyeama, Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire, da Ministan Muhalli, Sharon Ikeazor.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar da babban jami’in hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Honarabul Abike Dabiri-Erewa su ma za su kasance cikin tawagar.

Ana sa ran shugaba Buhari zai dawo Najeriya ranar Asabar.

Leave a Reply