Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jinjina wa ‘yan sandan Jihar Kano game da gano wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar mai shekara biyar tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyayenta.
Wata sanarwa da Garba Shehu mai magana da yawun shugaban ƙasar ya fitar a yau Juma’a ta ce Buhari ya ce yana fatan “hakan zai sa ‘yan ƙasa su ƙara amincewa da ayyukan jami’an tsaro”.
“Shugaba Buhari ya ce iyaye da kuma ‘yan Najeriya da suka dinga bin sawun halin da Hanifa ta shiga sun yi ta fatan za a ceto ta a raye, yana mai cewa aikin gano mutanen da jami’an tsaro suka gudanar da ya kai ga gano gawarta abin a yaba ne…abu ne da ya kamata ya sa mutane su ƙara yarda da mahukunta,” in ji sanarwar.
“In aka samu irin wannan abin alfaharin sai mutane su dinga yabon jami’an tsaro,” a cewar Buhari, wanda ya yi addu’ar Allah ya ji ƙan ta, sannan ya bai wa iyayenta haƙuri game da “baƙin cikin rashinta”.
A ranar Alhamis ne dai aka gano gawar Hanifa bayan wani malamin makarantarsu ya sace ta a watan Disamba sannan ya kashe tare da binne ta a ɗaya daga cikin gine-ginen makarantar.
Tuni mutumin ya amsa laifinsa a hannun ‘yan sanda sannan kuma gwamnatin Jihar Kano da ke arewacin asar ta rufe makarantar.