Boko Haram sun bude wuta kan jirgin yaƙin soji, sun kashe mutane 10

0
544

Labari daga Fatima Hassan GIMBA, Abuja

Boko Haram din sun bude wuta ne kan jirgin yaki mai saukar ungulu a Borno.

Mayaƙun ƙungiyar Boko Haram da ke samun goyon bayan kungiyar IS a yankin yammacin afirka (ISWAP), wanda ake kira Jamā’at Ahl as-sunnah lid-Da’wah wa’ll-jihād, sun bude wuta kan wani jirgin yaƙi me saukar ungulu, na rundunar hadin gwiwa ta multinational Joint Task Force (MNJTF).

Ku tuna cewa, MNJTF dai wata hadaddiyar rundunar soji ce ƙasa da kasa wanda ya hada kasashen Benin, Kamaru, Chadi, Nijar da kuma Najeriya.

Hedikwatar ta na N’Djamena, an yi mata lasisi da basu damar harbi da kawo karshen ta’addancin Boko Haram ta ko wane lamari.

Kazalika, an samar da irin rundunonin a sassa hudu na kasa: sashi na 1 (Cameroon) mai hedikwata a Mora; sashi na 2 (Chad) mai hedikwata a Baga-Sola; sashi na 3 (Nigeria) dake garin Baga; sashi na 4 kuma a (Niger) dake garin Diffa.

Wani rahoto ya nuna cewa, mayaƙun na amfani da muggan bindigu na kakkaɓo jiragen sama da GPMG, a yayin harin da suka kai kan jirgin, a ranar Alhamis din da ta gabata.

An bayyana mataimakin matuƙin jirgin a matsayin mutum guda da ya samu sauka jirgin cikin nasara, kuma ba tare da samun ko rauni ba.

Kungiyar Boko Haram da ya’yanta, daular Islama ta yammacin Afirka, sunyi kaurin suna wajen hare-haren ta’addanci.

Rundunar sojin Nijeria ta sha yin ikirarin cewa an yi galaba a kan ‘yan ta’addan, kuma a lokuta da dama tana yin watsi da duk wani hasara.

Rikicin Najeriya da ‘yan ta’addar Islama ya jawo hallaka kusan mutane 350,000 a karshen shekarar 2020, kamar yadda Hukumar raya kasashe ta majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ta bayyana a shekarar 2021.

Leave a Reply