Babu Farfesan da albashinsa yake kai shi wata – Farfesa Balarabe Abdullahi
“Babu Farfesan da albashinsa yake kai shi wata, sai dai idan ya haɗa da ƙwadago”. Farfesa Balarabe Abdullahi na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ne ya bayyana haka a hirarsa da gidan Rediyon Faransa (RFI).
KU KUMA KARANTA: Farfesa ya koma siyar da kayan miya saboda taɓarɓarewar tattalin arziki
Yanzu daga nan sai na tafi Jami’ar Gwamnatin tarayya dake Kashere a jihar Gombe, in tafi Jami’ar Gwamnatin jihar Yobe da ke dake Damaturu, na koyar, don a ba ni dubu ɗari biyu (200,000). Ka manta da lafiyarka, ka manta da rayuwarka ka bi hanyoyin Najeriya marasa kyau. Kullum ana cikin hatsari a hanyoyin, amma a haka za ka rufe ido ka tafi saboda albashinka ba ya isar ka.
Irina Farfesa na ƙure komai, a mataki na 10 nake (step 10). Ba zan iya saka ɗana a makaranta a Abuja ba, saboda albashina ba ya isa ta. Shi ya sa za ka ga wasu Malaman suna guduwa ƙasashen waje. Ni ma na samu koyarwa a South Korea, amma na ce ba zan je ba.
Amma Malaman jami’o’in kudancin ƙasar nan suna ta guduwa ƙasashen waje. Suna zuwa inda aka san darajarsu.
Ba ƙaramin aiki ba ne mutum ya zama Farfesa. Amma Farfesa ɗin nan a Najeriya ya fi zama wulaƙantacce. Aikin mu fa ba koyarwa ne kaɗai ba, koyarwa ne da bincike. Sannan a wata ɗin ma sai a yi kwanaki 40 ba a biya mu albashi ba.
Farfesa ɗan’uwanka zai zo wajenka yana hawaye, yana cewa rabon da a ɗora abinci a gidansa tun shekaranjiya. Malaman FCE da Federal Poly sun fi mu albashi. Chief Lecturer a College of Education ya fi ni albashi da dubu ɗari biyu (200,000). Wace irin gwamnati ce a Najeriya?









