Connect with us

Labarai

Aƙalla mutum ’87’ aka sace a Kajuru na jihar Kaduna

Published

on

Wasu ƴan bindiga a Najeriya sun yi garkuwa da aƙalla mutum 87 da suka hada da mata da yara a jihar Kaduna, kamar yadda mazauna garin da ‘yan sanda suka bayyana a ranar Litinin.

Kakakin rundunar ƴan sandan Kaduna Mansur Hassan ya tabbatar da faruwar lamarin, wanda ya ce ya faru a ƙauyen Kajuru a daren Lahadi amma bai iya bayyana adadin waɗanda suka ɓata ba.

Wani hakimin ƙauyen, Tanko Wada Sarkin ya ce an sace mutum 87. “Ya zuwa yanzu mun sami labarin dawowar mutane biyar da suka koma gida da suka tsere ta cikin daji,” kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho.

Sace mutane da gungun masu aikata laifuka ke yi don neman a biya su kudin fansa ya zama ruwan dare kullum a Nijeriya, musamman a arewacin kasar, inda ake ganin hukumomi ba su da ikon hana su.

KU KUMA KARANTA: Ƴan bindigar da suka sace ɗalibai 286 sun buƙaci kuɗin fansa naira biliyan ɗaya

Wasu rahotannin sun ce ɓarayin sun kuma fasa shaguna da gidajen mutane suka yi sata.

Shi ma shugaban ƙaramar hukumar Kajuru Ibrahim Gajere ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa ƴan bindigan sun kutsa garin da misalin karfe tara na dare a ranar Lahadi.

Ya kuma koka kan yadda ake yawan satar mutane a Kajuru a baya-bayan nan, lamarin da ke sanya mutane cikin tsoro da fargaba sosai.

Ko a ranar 7 ga Maris, an sace daliban wata firamaren gwamnati 287 da hedimasta da wasu ma’aikata a karamar hukumar Kuriga a jihar Kaduna. Masu garkuwa da mutanen na neman kudin fansa domin su sako daliban a cewar hukumar makarantar.

Sai dai a ranar Asabar shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi gargadi game da biyan kudin fansa ga ‘yan fashi ko ‘yan ta’adda ko kuma masu dauke da makamai domin a sako mutanen da aka sace.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Yarjejeniyar Auren Jinsi: Gwamnatin Najeriya za ta kai jaridar Daily Trust kotu

Published

on

Yarjejeniyar Auren Jinsi: Gwamnatin Najeriya za ta kai jaridar Daily Trust kotu

Yarjejeniyar Auren Jinsi: Gwamnatin Najeriya za ta kai jaridar Daily Trust kotu

Daga Idris Umar, Zariya

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta maka jaridar Daily Trust a kotu, tare da shigar da ƙorafi game da ita, a gaban ƙungiyar masu gidajen jarida ta Najeriya saboda abin da ta ƙira ”yaɗa kalaman neman tayar da rikici da karya aikin jarida”

Ministan yaɗa labaran Najeriya, Mohammed Idris ya ce gwamnatin tana sane da yadda a cikin ‘yan watannin baya, jaridar Daily Trust ke yaɗa labaran da ke neman gogawa gwamnatin kashin kaji.

Da ya ke magana a wajen wani taron manema labarai a ranar Asabar, ministan yaɗa labaran ya kafa hujja da labaran da jaridar Daily Trust ta wallafa a game juyin mulkin Nijar, da wanda ya ce jaridar ta rubuta a kan shirin sauya sunan titin Murtala Muhammad da ke Abuja zuwa Wole Soyinka da kuma na baya bayan nan a game da sanya hannu a kan yarjejeniyar da ta shafi amincewa da auren jinsi.

KU KUMA KARANTA: Alaƙar soyayya tsakanin jinsi ɗaya ta haramta a Iraƙi

Ya yi bayanin cewa a dukkan labaran, gwamnatin ta gano yadda jaridar ta bayar da rahoto ba tare da gabatar da hujja ko shaidun zargin da ta yi ba, lamarin da kuma gwamnatin ke kallo a matsayin wani yunƙuri na wallafa ƙarya domin tunzura jama’a.

Ya ce: ‘’Ba mu taɓa tunanin Daily Trust da mutanen da ke da ita za su kai wannan mataki ba wajen neman tayar da rikici a ƙasar nan, ta hanyar zargin cewa gwamnati ta sanya hannu a kan yarjejeniyar tallata auren jinsi. Wannan tsabar zalunci ne saboda babu wannan tanadi a cikin yarjejeniyar.’’

Ministan ya koka da yadda wannan labarin ya janyo huɗuba mai zafi daga wasu malaman addini da kuma jefa jama’a cikin halin ɗarɗar, wanda kuma ya ce jaridar ce ta janyo.

KU KUMA KARANTA: Malaman addini a Malawi sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da auren jinsi

Saboda haka, ministan ya ce ‘’Gwamnatin tarayya za ta bi duk hanyoyin da doka ta amince da su, domin neman haƙƙi a kotu.’’

Continue Reading

Labarai

Gwamnan Neja ya ba da umarnin a mari malamin addini (Bidiyo)

Published

on

Gwamnan Neja ya ba da umarnin a mari malamin addini (Bidiyo)

Gwamnan Neja ya ba da umarnin a mari malamin addini (Bidiyo)

An jiyo Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja yana ba da umarnin jami’an tsaronsa da su yi wa wani malamin addinin Islama cin mutunci a yayin bikin addu’ar Fidda’u ga matar mataimakinsa, Hajiya Zainab Yakubu Garba da ta rasu.

Lamarin wanda ya auku a Minna a ranar Juma’a, ya auku ne a lokacin da malamin ya sadaukar da kansa domin gudanar da addu’a, lamarin da aka ce ya harzuƙa Gwamna Bago.

A cikin faifan bidiyon, ana iya jin Gwamna Bago yana jawabi ga masu jajantawa, inda ya nuna cewa za a iya gudanar da addu’o’i ga marigayiyar a cikin gida, kafin daga bisani ya fusata a lokacin da malamin ya fito.

KU KUMA KARANTA: Allah Ya yi wa matar mataimakin gwamnan Neja rasuwa

Ya tuhumi malamin, sannan ya umurci jami’an tsaronsa da su ɗauki mataki, inda ya umarce su da su yi masa mari mai kyau sannan su kama shi.

Shaidu da suka halarci taron sun nuna kaɗuwa dangane da wannan hali na gwamnan, inda suka yi la’akari da irin tsaurin ra’ayinsa ga malamin.

Wannan lamari dai ya ƙara rura wutar zarge-zargen da ke tattare da yadda Gwamna Bago ke da alaƙa da cin zarafi ga mataimaka da magoya bayansa, kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito kuma majiyar gwamnan ta tabbatar.

Kalli bidiyon a nan:

Continue Reading

Labarai

ECOWAS na shirin ƙaddamar da kuɗin bai ɗaya da zai yi aiki a ƙasashen ƙungiyar

Published

on

ECOWAS na shirin ƙaddamar da kuɗin bai ɗaya da zai yi aiki a ƙasashen ƙungiyar

ECOWAS na shirin ƙaddamar da kuɗin bai ɗaya da zai yi aiki a ƙasashen ƙungiyar

Ministocin kuɗi da Gwamnonin manyan Bankunan ƙasashen ƙungiyar raya tattalin arzikin Yammacin Afirka 15, sun ci gaba da shirye-shiryen ƙaddamar da kuɗin bai ɗaya da aka yiwa laƙabi da ECO.

Wannan yunƙuri da ke da nufin haɓaka tattalin arziƙi yankin Afirka ta Yamma, ya samu amincewar tarayyar Najeriya.

A wata sanarwa da ma’aikatar kuɗi ta Najeriyar ta fitar jiya juma’a, ɗauke da sa hannun Daraktan watsa Labarai, Mohammed Manga, ta ce Ministan Kuɗin ƙasar Wale Edun, ya lura da muhimmiyar rawar da kuɗin na bai ɗaya zai taka wajen bunƙasa ci gaban tattalin arziƙi, da kuma ci gaban yankin baki ɗaya.

KU KUMA KARANTA:ECOWAS na buƙatar dala biliyan 2.6 duk shekara don kafa rundunar tsaro – Badaru

Edun, ya kuma jaddada ƙudirin Najeriya na ci gaba da shiga gaba wajen aiwatar da shi, wanda ake ganin wani ɓangare ne daga shirin hukumar yin katin ɗan ƙasa na samar da kati guda mai amfani a wurare uku, wanda ake sa ran zai fara aiki a watan Agusta mai zuwa.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like