Connect with us

Kannywood

Aurenmu da Sani Danja: Ina bai wa masoyan mu haƙuri -Mansurah Isah

Published

on

Daga Saleh INUWA, KANO


A karon farko tun bayan rabuwar auren Sani Danja da Mansurah Isah, yau kusan shekara 1 da rabi kenan, Mansurah Isah ta fito ta yi magana a game da mutuwar auren na su.
A wata tattaunawa da Mujallar fim tayi da ita a ‘Yan ƙwanakinnan, Mansurah Isah ta bayyana cewar, tun bayan rabuwar su da Sani Danja ta ke ganin labarai Kala Kala a game da rabuwar ta su, wasu su na zagi, wasu su na nuna ɓacin ran su a game da rabuwar da suka yi, wadda Kuma komai ƙaddara ce daga Allah.


Ta ce “Ko da farko ma abin da ya sa ta sanar da rabuwar su a Soshiyal Media, ta yi Hakan ne domin a matsayin ta na Fitacciya kada a ganta a wani waje ko ta tsaya da wani a rinƙa yi mata kallon ta na yin wasa da aure, don haka ta sanar da duniya.


Ta Ƙara da cewar “Na san mutane su na sha’awar zaman auren mu har ma a na kafaisali da mu a cikin ‘Yan fim da muka shafe tsawon lokaci mu na zaman aure, don haka rabuwar ba ta yi wa kowa daxi ba. To Amma mutane su sani duk rashin jin dadin su mu mun fi su rashin jin dadin hakan saboda mu ne mu ke zaune da juna kuma muka rabu.

Mutane su sani ba mun yi aure ba ne don mu rabu. Domin idan mun yi ne don mu rabu, babu yadda za a yi mu shafe shekaru 14 muna tare, don haka Allah Ne ya kawo ƙarshen zaman mu.


Kuma duk son mu da zama tare idan aka kawo wajen da zama ya haramta, to dole a yi hakuri da juna, don haka kamar yadda mutane su ke nuna mana so da ƙauna, kuma su ke yi mana fatan alheri, mu ma muna yi musu fatan alheri, kuma ina ba su hakuri da ƙaunar da su ke nuna mana. Masu zagi kuma su je su yi ta yi ba za mu Hana su ba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Kannywood

Kannywood ta ba wa Hisbah tabbacin goyon baya a Kano

Published

on

Bayan ce-ce-ku-ce, Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sake zama da daraktoci da furdusoshi da jarumai da sauran masu ruwa da tsaki a Kannywood don tsaftace harkar fim da nufin kau da ayyukan baɗala a jihar.

A jawabansu daban-daban, Shugaban Ƙungiyar MOPPAN ta Ƙasa Dokta Ahmad Sarari da takwaransa na Jihar Kano Ado Ahmad Gidan Dabino da Shugaban Ƙungiyar Jarumai Alasan Kwalle sun nuna jin daɗinsu game da taron inda suka sha alwashin ba wa Hisbah goyon baya tare da alkawarin cewa nan gaba za a samu gyara a harkar fim ɗin.

Wannan shi ya kawo ƙarshen ce-ce ku-cen da aka yi ta yi game da ganawar Hukumar da ’yan fim na farko, wanda mafi yawansu suka ƙaurace wa bisa hujjar cewa Hisbar ba ta bi hanyar da ta dace wajen gayyatar su ba.

KU KUMA KARANTA: ’Yan Kannywood da dama sun ƙaurace wa taron da Hisbah ta gayyata a Kano

Hukumar ta sake miƙa musu goron gayyata a karo na biyu wanda suka amsa a ƙarƙashin jagorancin ɗan gidansu wato Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano Abba Almustapha.

Kwamanda-Janar na Hukumar Hisbah Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa ƙorafe-ƙorafe da suke yawan samu daga Kanawa da sauran sassan Najeriya kan yadda ’yan fim ke nuna abubuwan da suka saɓa wa addinin Musulunci da al’adun Hausawa a cikin finafinansu ya sa suka ga dacewar zama da masu ruwa da tsaki a harkar fim don laluɓo hanyoyin kawo gyara a cikin harkar.

“Ita Hukumar Hisbah an kafa ta ne don ta saita al’umma a kan koyarwar addinin tare da yi musu katanga daga aikata munanan ayyuka.

“Muna so a laluɓo hanyoyin da za a rage nuna abubuwa da suke na tir tare da ci gaba da nuna abubuwa da za su dabbaka addinin da kyawawan koyarwar al’adun Hausawa a harkar fim,” in ji Daurawa.

A nasa ɓangaren, Abba Almustapha ya bayyana cewa tuni ’yan fim din suka amince za su zama masu bin doka.

Abba Almustapha ya jaddada cewa nan ba da dadewa ba hukumomin biyu za su shirya taron ƙara wa juna sani da ’yayan Kannywood don ilimintar da su kan abin da ya shafi fim ta fuskar addinin Musulunci inda za a gayyato fitattun malaman Musulunci don tattauna tare da laluɓo hanyoyin da za a kai harkar fim ɗin ga tudun mun tsira.

Continue Reading

Kannywood

Ɗan wasan ƙwallon ƙafa Ahmed Musa, ya cika alƙawari, ya sayawa Karkuzu gida

Published

on

Kamar yadda Neptune Hausa ta kawo labarin cewa shahararren ɗan wasan Nijeriya Ahmed Musa MON ya yi alƙawarin sayawa Baba Karkuzu gida a yau Talata, alƙawari ya cika.
Alhamdulillah an sayi gida an kuma karɓi takardun gidan.

Kamar yadda kuke gani a hoto Baba Karkuzu ne riƙe da Jessy ɗin Ahmad Musa tare da takardan gidan shi cikin farin ciki da godiyar Allah (T).

Jarumin Kannywood, Karkuzu ya makance, yana kukan neman taimako

Ga waɗanda suka taimaka, Baba yace a isar masa da godiya a gare su, Ubangiji Allah ya sakawa kowa da alkhairi, Allah ya biyawa kowa buƙatar shi, wanda suka taimaka kuɗi da wanda suka taimaka da addu’a.

Dukkan mu Allah ya sakawa kowa da gidan Aljannah, Allah ya dube mu lokacin da muke cikin tsanani, Allah ya suturta mu da suturar shi mara yankewa, Allah ya rufa mana asirin mu. Ameen ya Allah.

Continue Reading

Kannywood

Jarumin Kannywood, Karkuzu ya makance, yana kukan neman taimako

Published

on

Fitaccen jarumin Kannywood, Abdullahi Shuaibu wanda aka fi sani da Karkuzu ya makance kuma yana fama da rashin lafiya.

Jarumin, wanda aka yaɗa bidiyonsa a shafukan sada zumunta, ya nemi taimakon kuɗi, inda ya bayyana cewa ya yi rashin lafiya tun watan Disambar 2020.

Shuaibu ya fara fitowa a masana’antar nishaɗantarwa ta Hausa a shekarun 1980 tare da shahararriyar wasan kwaikwayo mai suna Karkuzu na Bodara wanda ya sanya ake masa laƙabi da Karkuzu.

A zantawarsa da wannan jarida bayan faifan bidiyo, Karkuzu ya ce, “Yanzu na makance kamar yadda nake magana da ku. Ina matuƙar buƙatar taimakon kuɗi. Ba ni da abincin da zan ci da ciyar da iyalina.

KU KUMA KARANTA: Yadda mutuwar Alhaji Mala na shirin ‘Daɗin Kowa’ ta jijjiga Kannywood

“Gidan da nake zaune yanzu za a sayar. Idan sun sayar da wannan gidan, ban san inda zan dosa ba. Don haka ne nake neman taimako daga ‘yan Najeriya da su kawo min agaji.

A ƙalla ‘yan Najeriya su taimaka min sayan wannan gidan da nake zaune.”

Dangane da makanta, ya ce, “An min aiki sau biyu, amma a ƙarshe likitoci sun ce glaucoma ce, kuma ba zan sake gani ba. Na yarda da hakan a matsayin makoma ta. Amma ya kamata ‘yan Nijeriya su taimake ni. Kawo min gidan nan, da abinci.”

Masana’antar Kannywood na da ƙungiyoyi da dama, amma akwai zargin cewa ‘yan wasan kwaikwayo da dama ba sa kula da su idan ba su da lafiya kuma suna buƙatar taimako.

Zuwa haɗa wannan rahoto, ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Najeriya Ahmad Musa ya ba shi kyautar naira dubu ɗari biyar, sannan ya ce a nemo gida na naira miliyan biyar zai saya masa.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like