Atiku ya tallafawa ‘yan kasuwar Kantin kwari da Naira miliyan Hamsin

0
264

Daga Shafaatu DAUDA, Kano

Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen baɗi na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, ya bai wa ƴan kasuwar Kantin Kwari tallafin naira miliyan 50.

Tallafin nasa dai a matsayin gudunmawa bisa iftila’in ambaliyar ruwan sama da kasuwar ta fuskanta a kwanakinnan.

Atiku Abubakar, ya sanara da bada tallafin ne yau Litinin a gidan Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau da ke unguwar Munduɓawa a Kano.

Kasuwar ta Kantin Kwari na daga cikin wuraren da suka gamu da iftila’in ambaliyar ruwan wadda wasu sassan jihar Kano da dama suka fuskanta.

Leave a Reply