ASUU za ta ware rana ɗaya don yin zanga-zangar lumana

1
525

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ta ce za ta ayyana ranar da ba za ta shiga aji ba a jami’o’in ƙasar domin bayyana rashin jin daɗinsu game da zargin da take yi wa gwamnatin tarayya na riƙe musu albashin wasu watanni.

Babban jami’in ƙungiyar mai lura da shiyyar Kano Farfesa Abdulkadir Muhammad ya shaida wa BBC cewa ƙungiyar ASUU ta yanke shawarar ne domin bayyana ɓacin ranta kan matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na ƙin biyan mambobin ƙungiyar albashinsu na wasu watanni bayan sun janye yajin aiki.

Ya ce ”kowane reshe zai zaɓi rana guda da zai gudanar da taro tare da zanga-zangar lumana, domin nuna ɓacin ransu da rashin jin daɗinsu kan yadda gwamnatin tarayya ke ƙoƙarin mayar da malaman jami’o’i ma’aikatan wucin gadi”.

Ya ƙara da cewa ”ASUU za ta gudanar da taro a kowane reshe na ƙungiyar, inda kuma duka mambobin ƙungiyar za su hallara, bayan gabatar da laccoci a wajen taron, mambobin ƙungiyar za su gudanar da zanga-zangar lumana a cikin kowacce jami’a, sannan kuma a ranar ba za su shiga aji domin koyawa dalibai karatu ba’.

A cikin watan Oktoba ne ASUU ta janye yajin aikin da ta kwashe wata takwas tana gudanarwa.

1 COMMENT

Leave a Reply