Ana zargin wani matashi da kashe mahaifiyarsa a Bauchi

0
13
Ana zargin wani matashi da kashe mahaifiyarsa a Bauchi

Ana zargin wani matashi da kashe mahaifiyarsa a Bauchi

Daga Umar Idris, Zariya

Wani matashi mai suna Safiyanu Dalhatu, da ke unguwar Abujan Kwata a cikin garin Bauchi.

Matashin ya yiwa mahaifiyar tasa dukan Kawo wuka da yayi sanadin kasheta har lahira mahaifiyar mai suna Salama Abdullahi, mai shekara kusan 45 a duniya.

Shi dai Safiyanu ana tuhumarsa da ɗaukan babban taɓarya inda ya yi ta dukan mahaifiyar da ta haifeshi da ita a hannayenta da sauran sassan jikinta, lamarin da ya janyo mata munanan raunuka.

Wannan abun tir da kaito ɗin ya faru ne a ranar 24 ga watan Fabrairun 2025 wajajen ƙarfe uku na rana, inda mambobin ‘Yan kwamitin tsaro na unguwa suka kai rahoton faruwar lamarin ga caji ofis ɗin ‘yansada ta ‘A’ Divisional.

Bayan samun rahoton, babban baturen ɗansa da ke caji ofis ɗin, CSP Abdullahi Muazu ya jagoranci tawagar ‘yansanda zuwa gidan da abun ya faru tare da hanzarta kai wacce aka jikkatar zuwa asibitin koyarwa ta (ATBUTH) da ke Bauchi domin ƙoƙarin ceto rayuwarta.

Amma abun takaici, likita ya tabbatar da mutuwarta.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya fitar a ranar Talata, ya ce, binciken farko-farko ya nuna saɓani ne ya shiga tsakanin ɗa da uwar tasa lamarin da ya janyo shi ɗan yi ma ta dukan kawo wuƙa.

“Wanda ake zargin an cafke shi, sannan taɓaryar da ya yi amfani da ita wajen aika-aikar an kwatota a matsayin hujja,” sanarwar ta shaida.

Kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi,
CP Auwal Musa Mohammed, ya umarci sashin binciken manyan laifuka (SCID) da su zurfafa bincike kan lamarin..

KU KUMA KARANTA:‘Yansanda a Bauchi, sun cafke magidanci da ya lakada wa matarsa duka ta mutu har lahira

A cewar sanarwar da zarar aka kammala gudanar da bincike za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu domin fuskantar laifinsa da ake zarginsa a kai.

Bincike ya nuna cewa, shaye-shaye ne matashin ke yi inda ita kuma mahaifiyar tasa ta masa faɗa da ya daina lamarin da ya fusata shi ya kamata da duka.

Ta ce: “Abun da ya faru wai shi yana ɗan shaye-shaye ne bayan ya dawo daga makaranta ta zo tana masa faɗa sai ya ce baya so ita kuma ta cigaba da masa faɗa, sai ya ɗauko muciya ya yi ta kwaɗa mata tana ta ba shi haƙuri amma an rasa wanda zai zo ya hana shi dukanta a lokacin.

“Yana ta dukanta sai abokansa suka zo, bayan da suka shigo gidan sai suka kamashi suka yi ta masa duka. Dukan da yaron ya mata shi ne ya janyo ta yanki jiki ta faɗi.

“Tun kafin a kaita asibiti ma rai ya yi halinsa. Ba ka ga jikinta ba ne, kanta duk jini, ya karya mata hannu, haka muka ga hannunta a juye kai duk jini. Ya mata raga-raga,” majiyarmu ta shaida.

Leave a Reply