Daga Wakilinmu
Wakilan jam’iyyar APC daga sassa daban-daban na Najeriya sun amince da tsohon gwamnan jihar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban jam’iyyar da ke mai mulkin kasar.
Gwamnan Jigawa Muhammadu Badaru ne ya sanar da hakan a yayin babban taron jam’iyyar bayan duka waɗanda suke takara sun janye wa Abdullahi Adamu.
Sanata Abdullahi Adamu, wanda da farko ba ya cikin waɗanda suka nuna sha’awar takarar shugabancin APC, daga bisani ya kutso kuma ya samu goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari da wasu gwamnoni.
Wannan goyon bayan ne ya tilasta wa sauran ƴan takarar shugabancin APC janye wa a ranar Asabar kafin shiga dandalin taron.
Ƴan takarar da suka janye sun da tsohon gwamnan Benue George Akume da tsohon gwamnan Nasarawa Tanko Al-Makura da tsohon gwamnan Zamfara Abdul’Aziz Yari Abubakar da Saliu Mustapha d kuma Etsu Muhammed.
Sanata Adamu ya zama sabon shugaban APC ne fiye da shekara guda bayan sauke tsohon gwamnan jihar Edo Adams Oshiomhole daga mukamin da kuma nada Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe a matsayin shugaban kwamitin riko na jam’iyyar.
Abdullahi Adamu yanzu haka shi ne Sanatan da ke wakiltar Nasarawa ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya kuma sau biyu yana zama gwamna a jihar ta Nasarawa.
Ya rike mukamin gwamnan jihar Nasarawa ne daga sekarar 1999 zuwa 2007. Hasalima shi ne gwamnan farar-hula na farko a jihar.
An haife shi a garin Keffi da ke jihar Nasarawa kuma ya yi karatunsa na firamare da Sakandare a jihar Nasarawa da kuma Benue ta yanzu a daga 1960 zuwa 1962.
Ya kuma yi karatun gaba da Sakandare a Kwalejin Fasaha, Bukuru, da kuma Kwalejin Fasaha da ke Kaduna wato Kaduna Polytechnic inda ya samu Babbar Difiloma.
A shekarar 1992, ya kammala Digirinsa na farko a fannin Lauya a Jami’ar Jos kuma ya zama lauya a 1993.
Sanata Adamu ya soma siyasa a 1977, kuma ya rike mukamai da dama.
Ga abubuwa shida da suka kamata ku sani game da sabon shugaban jam’iyyar APC:
- Yana cikin wadanda suka kafa jam’iyyar PDP a 1998 wadda ta mulki Najeriya tsawon shekara 16
- Ya rike mukamin gwamnan jihar Nasarwa na farar-hula na farko daga 1999 2007 a karkashin jam’iyyar PDP. Bayan ya kammala wa’adinsa na gwamna, an zabi Abdullahi Adamu a matsayin Sakataren Kwamitin Amintattu na PDP.
- Shi ne shugaban farko na kungiyar gwamnonin Najeriya daga 1999 zuwa 2004.
- Ya fita daga PDP a 2013 inda ya shiga jam’iyyar APC kasa da shekara daya bayan kafa ta. Yana cikin mambobin Sabuwar PDP da suka narke suka kafa APC.
- Ya zama Sanatan da ke wakiltar Nasarawa ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya
- A shekarar 2010, hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najerita ta’annati ta zari Abdullahi Adamu da mutum 18 da yin zambar N15 bn.
Gabanin babban taron jam’iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu ya shaida mana cewa ba ya tsoron fafatawa da kowanne dan takara a zaben shugabancin jam’iyyar yana mai cewa “ban taba faduwa zabe ba don haka ba na shakkar kowa”.
Ya ce a matsayin sa na mutumin da ya jagoranci kwamitin sulhu na jam’iyyar, shi ne ya fi sanin kalubalen da ke gaban jam’iyyar da kuma yadda za a shawo kansu.
Sai dai masu sharhi a kan harkokin siyasa na cewa akwai babban kalubale a gaban tsohon gwamnan na jihar Nasarawa ganin yadda ake zargin cewa wasu daga cikin ‘yan takarar sun amince su yi maslaha ne kawai saboda babu yadda za su yi.
Baya ga haka, jam’iyyar ta APC na fuskantar babban kalubale a zaben 2023 sakamakon zargin da wasu ‘yan kasar ke yi cewa ba ta cika galibin alkawuran da ta daukar musu ba, ko da yake jam’iyyar ta sha cewa tana bakin kokarinta.