An Yaba Wa Dokta Sabo Saboda Bunkasa Karamar Hukumar Bichi

0
362


JABIRU A HASSAN, Daga Kano.
Al’umar Karamar hukumar Bichi, sun jinjinawa Shugaban Karamar hukumar Dokta Yusuf Muhammad Sabo Saboda kokarin da yake yi wajen kyautata rayuwar al’uma ta hanyoyi daban-daban, tareda samar da yanayi mai kyau na zamantakewa.
A cikin wasu sakonni da al’umar yankin suka gabatar wa wakilin mu, sun sanar da cewa ko shakka babu Dokta Sabo Yana bakin kokarin sa wajen ganin kowane bangare na fadin Karamar hukumar Yana rabauta daga wani abu domin kyautata rayuwar al’uma batare da nuna bambanci ba.
Haka kuma dukkanin wadanda suka yi bayanai a cikin sakon sun bayyana cewa daga lokacin da aka zabi Dokta Yusuf Muhammad Sabo bai zauna ba yana ta kokarin ganin al’umar sa suna amfana da wasu abubuwa na kyautata zamantakewa duk da cewa duniya tana cikin wani yanayi na kalubalen tattalin arziki.
Wakilin mu ya duba yadda majalisar Karamar hukumar ta Bichi bisa jagorancin Dokta Yusuf Muhammad Sabo ke kokarin bunkasa wannan yanki,tareda jin yadda wadannan abubuwa da Karamar hukumar keyi zasu taimaki rayuwar al’uma, musamman a wannan lokaci na bukatar hanyoyin dogaro dakai domin yin rahoto na musamman a kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here