An kama malami kan lalata da ɗaliba a Jami’ar Nsukka

0
89

Rundunar ‘yan sandan Jihar Enugu ta kama malamin Jami’ar Najeriya ta Nsukka (UNN) Mista Mfonobong Udoudom, bisa zarginsa da laifin cin zarafin ɗalibarsa.

Tuni dai hukumar makarantar ta dakatar da lakcaran bayan tabbatar da faruwar lamarin a iya binciken da ta gudanar.

Wakilinmu ya ruwaito cewa ‘yan sanda sun kama malamin ne jim kaɗan bayan hukumar jami’ar ta dakatar da shi a daren ranar Talata.

Wani faifan bidiyo da aka yi ta yadawa  a daren ranar Litinin, ya nuna  Udoudom yana ta ƙoƙarin maida gajeren wandonsa jikinsa bayan an kama shi yana yunƙurin lalata da ɗalibarsa.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta tsare mai gidan haya kan lalata da ’yar shekara 6 a Ibadan

Wata majiya mai ƙarfi da ta buƙaci a sakaya sunanta ta bayyana cewa, ba wannan ne karo na farko da aka taɓa zargin Mista Udoudom da yunƙurin lalata da ɗalibansa ba a jami’ar.

An ce malamin ya yi barazanar kada ɗalibar a darasin da yake ɗaukarsu muddin bata miƙa kanta gare shi ba.

Hoton bidiyon da ya yi ta yawo a kafar intanet ya nuna malamin yana ƙoƙarin sanya gajeren wandonsa, a cikin ofishinsa, inda ake zaton a nan ya so ya yi lalata da ɗalibar.

Mukaddashin jami’in hulɗa da jama’a na Jami’ar, Dakta Okwun Omeaku ne bayyana dakatar da shi a daren ranar Talata.

Ya ce, “Wannan dakatarwa ce ta kai tsaye ba tare da ɓata lokaci ba,  hukumar jami’a ta buƙaci kwamitin ladabtarwa ya binciki lamarin.

“Ina so jama’a su ƙara sanin cewa, Jami’ar Najeriya ta Nsukka ba ta da haƙuri game da lalata daga ma’aikata zuwa ga dalibai. UNN na daga cikin jami’o’in kasar nan da ke da zafin hukunci kan cin zarafin mata.

“A matsayinmu na jami’a, mun himmatu wurin kare dalibanmu daga duk wani nau’i na cin zarafi , kuma Hukumar Kula da Jami’ar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin  hukunta Mista Mfonobong David Udoudom, kamar yadda ka’idojinmu suka tanada, idan kwamitin ladabtarwar mu ya same shi da laifi.”

Leave a Reply