An haifi yara ‘yan biyu maza a haɗe a Sakkwato

0
171

Daga Maryam Umar Abdullahi

An haifi yaro namiji, a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, wanda ya zo da gangar jiki daya, da kai biyu, idanu huɗu, baki biyu da kuma hanci biyu.

Duk da yake abu ne wanda ba sabon abu ba, amma wasu lokuta ana samun labarin haihuwar yara ‘yan biyu ko ‘yan uku waɗanda ake haihuwa a haɗe, ko kuma wani sashe na jikin su haɗe, kamar yadda aka yi ta samu a ƙasashen duniya.

Wannan karon ma an haifi yaro namiji, a jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya, wanda ya zo da gangar jiki ɗaya, da kai biyu, idanu huɗu, baki biyu da hanci biyu.

A ranar Talata, 30 ga watan Janairun wannan shekara ne aka kai mahaifiyar yaron a asibitin mata da ƙananan yara da ke tsakiyar garin Sakkwato da matsalar juna biyu, kuma ya kai lokacin haihuwa, sai bincike ya nuna da wuya ta iya haihuwar abin da ke cikinta.

KU KUMA KARANTA:Tsohon gwamnan Yobe, Bukar Abba Ibrahim, ya rasu

Ɗaya daga cikin ma’aikatan asibitin da suka yi fama da matar, Hafsat Muhammad Bazza, ta ce hoton cikin da aka yi ya nuna cewa jaririn da ke cikin mahaifar matar yana da babban kai saboda haka ba za ta iya haihuwar sa da kanta ba, dole sai an yi aiki an fitar da shi, sai aka shiga da ita ɗakin tiyata.

A lokacin da aka yi mata aikin tiyata sai aka fitar da yaro wanda ba a saba ganin irin saba.

Maryam Yusuf Muhammad ɗaya daga cikin dangin mahaifan yaron kuma ɗaya daga cikin waɗanda ke hidima a asibiti lokacin haihuwar ta ce da aka fitar da yaron an tarar da yana da idanu huɗu, baki biyu da hanci biyu, kuma bayan sa a buɗe yake har ana ganin lakkar sa.

Mahaifin yaron Yusuf Abdullahi yana cike da al’ajabi ganin irin abubuwan da ake gani a wasu ƙasashe na duniya yau ga shi a gidan sa cikin iyalan sa, sai dai ya yi godiya ga Allah kuma ya nemi taimakon yadda zai iya kulawa da yaron.

Masana kiwon lafiya Dakta Umar Idris, likita ne a Sakkwato, ya ce ana samun irin wannan lamarin kaloli mabambanta kuma yana faruwa ne a lokacin da ake halittar ‘yan biyu, idan aka samu tsaiko wajen rabuwar su tun a cikin mahaifa.

A cewar masanin kiwon lafiyar babu abu ɗaya da za’a ce shi ke haifar da hakan amma dai akwai wasu abubuwa da za’a ce su ne silar samar da hakan, waɗanda suka haɗa da yanayin halitta na zuri’a, ko yanayin muhallin da suke ciki ko kuma shaye-shayen magunguna barkatai irin na gargajiya, ga masu juna biyu.

Wasu lokuta idan aka samu hakan bincike kan iya nuna ko za’a iya raba yaran da aka haifa hade, ko akasin haka.

Leave a Reply