An ga watan sallah a Saudiyya
An ga jinjirin watan Shawwal a Saudiyya wanda ke tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadana.
KU KUMA KARANTA:A fara duban watan Shawwal ranar Asabar – Sarkin Musulmi
Shafin Haramain na mahukuntan da ke kula da Masallatan Harami na Makkah da Madinah ne ya tabbatar da hakan.
Saboda haka, gobe Lahadi take Sallah ƙarama a ƙasa mai tsarki.