A fara duban watan Shawwal ranar Asabar – Sarkin Musulmi

0
170

A fara duban watan Shawwal ranar Asabar – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar, ya umarci al’umma da su fara duban watan Shawwal daga gobe Asabar, 29 ga watan Ramadan 1446, wanda ya yi daidai da 29 ga watan Maris, 2025.

Shugaban kwamitin harkokin addini na masarautar Sakkwato, Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce duk wanda ya ga jinjirin watan Shawwal ya sanar da Hakimi ko Uban Ƙasa mafi kusa da shi, domin a kai rahoto ga Sarkin Musulmi.

KU KUMA KARANTA:Daga fara Azumin Ramadan, mutane 11 ne suka musulunta a wajen tafsirin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Wazirin Sakkwato, ya yi addu’a Allah Ya taimaka musu a wannan muhimmin aikin na addini da suke yi.

Idan aka dace da ganin watan Shawwala a ranar Asabar, hakan na nufin za a yi sallah ƙarama a ranar Lahadi, akasin haka kuma za a yi sallah a ranar Litinin.

Yanzu haka dai al’ummar Musulmi sun mayar da hankali wajen shirye-shiryen bikin sallah ƙarama na bana.

Leave a Reply