Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin inganta aikin jarida a jihar

0
68
Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin inganta aikin jarida a jihar

Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin inganta aikin jarida a jihar

Daga Idris Umar, Zariya

A yunkurin ganin ta inganta kwarewa da walwalar yan jaridu, Gwamnatin Jihar Kano ta samar da kwamitin mutane Bakwai dai zai rika bayar da shawarwari da lura akan yadda ake gudanar da aikin jarida da jihar.

Kwamishinan Ma,aikatar Yada Labarai da Al,amuran Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana haka a lokacin taron buda baki na azumin watan ramadan, karo na farko a tarihin kungiyar Yan Jaridu a jihar Kano, wanda ya gudana a sakatariyar kungiyar da ke farm center.

Haka kuma, Kwamishinan ya bayyana shirye-shiryen Gwamnatin Jihar Kano na Kaddamar da Asusun Tallafawa Yan Jaridu a jihar domin samar musu kyakkyawan yanayin gudanar da aikinsu kamar yadda ya kamata.

Kwamitin Mutane 7 don bayar da shawarwarin akan Aikin Jarida a jihar Kano ya kunshi:

1. Alhaji Ahmed Aminu – Chairman
2. Alh. Mohammed Danyaro
3. Alh. Farouk Umar Usman
4. Hajiya Aisha Sule
5. Mallam Auwalu Mu’azu
6. Alh. Bello Sani Galadanchi
7. Comrade Suleiman Abdullahi Dederi – Secretary

Kwamishina ya kara da cewar Kwamitin zai taimaka wurin bunkasa aikin yan jarida a jihar.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Kano ta ba da umarnin cafke ‘yan jarida 2 kan wallafa wani rubutu

Da yake jawabi, shugaban kungiyar yan jaridu ta kasa reshen jihar kano, kwamared suleiman Abdullahi Dederi ya bayyana cewar wannan shi ne karo na farko da aka taba shirya taron shan buda baki da azumi a sakatariyar kungiyar.

Ya ce hakan na nuni da cewar akwai kyakkyawar alaka tsakanin yan jaridu da kuma ma,aikatar yada labarai ta jihar kano.

A jawabinsa Tsohon Babban Sakatare a ma’aikatar yada labarai ta jihar kano, Alhaji Ahmed Aminu ya bayyana cewar yan jaridu su na da muhimmiyar rawar takawa domin ganin an samu al,umma ta gari ta fuskar siyasa da tattalin arziki da addini da ma zamantakewa.

Ya koka yadda ake ci gaba da samun gibi mai girma a rashin kwarewar aiki ga yan jaridar wannan lokaci.

Shi ma a jawabinsa, Alhaji Muhammad Danyaro, tsohon babban sakataren maaikatar yada labarai, ya bayyana cewa aikin yan jaridu shi ne su sanar da al’umma ayyukan gwamnati da kuma sanya su a hanya yadda za su tafiyar da rayuwarsu, ya na mai cewar mafi yawanci yan jaridu basa sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

Ya bayyana horaswa a matsayin babbar dama ta bunkasa aikin jarida a jihar kano.

Ya kuma bukaci Gwamnati da ta inganta shirin horas da yan jaridu da kuma sojojin baka ta yadda za,a tsaftace aikin jarida daga masu cin zarafi ko kuma bata suna a kafafen yada labarai.

Shima a jawabinsa, Tsohon shugaban gidan rediyo kano, Alhaji Bello Sani Galadanci ya yabawa Kwamishinan yada labarai, saboda kokarin da ya ke yi domin ciyar da aikin jarida gaba.

Tunda fari Darakta a Gidan Rediyo Kano, Mallam Daiyabu Mai Mai Rano, ya bukaci yan jaridu da su ji tsoron Allah a yayin da su ke gudanar da ayyukan su.

Jinjina ga Kwamishinan ‘Yan Sanda da daukacin Jami’an tsaro a jihar Kano bisa jajircewarsu wajen gudanar da aiki

Idan yace kowanne mutum abin tambaya ne gobe kiyama akan abin da ya gudanar a rayuwarsa ta duniya.

Leave a Reply