An ceto wani mutum da aka kulle a ɗaki tsawon shekaru 20

0
567

An ceto wani dattijo mai shekaru 67, Ibrahim Ado, wanda aka kulle a ɗaki tsawon shekaru 20. Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ne suka ceto shi a ranar Laraba, 12 ga watan Oktoba. An gano mutumin ne tsirara kuma an kulle shi a ɗaki a wani gida da ke hanyar Bayajidda a Kaduna, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.

Mazauna gidan sun gudu a lokacin da tawagar ‘yan sanda suka isa gidan. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige ya shaidawa manema labarai cewa za a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Jalige ya ce wasu jami’an kiwon lafiya na muhalli ne da aiki yakaisu gidan suka fara gano mutumin mai suna Ibrahim Ado. “Sun kai rahoto ga sashin ‘yan sanda na Magajin Gari, kuma kwamishinan ‘yan sandan ya umurci jami’ai da su tafi da mutumin.

Ya ƙara da cewa, “Ya kuma ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin don bankaɗo al’amuran da suka shafi lamarin da kuma dalilin da ya sa aka keɓe mutumin na tsawon wannan lokaci,” in ji shi.

Jalige yace an kai wanda aka kashen asibiti domin a duba lafiyarsa.

Leave a Reply