Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.
SHUGABAN tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya kara jaddada kudirin Gwannati na yin kasuwancin hadin Gwiwa da masu zaman kansu, da nufin bunkasa tattalin arzikin kasa.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a wajen babban taron bude kasuwar duniyar kasa da kasa karo na 43 da ake yi a Kaduna.
Kasuwar duniyar dai cibiyar bunkasa kasuwanci,ma’adanai,masana’antu da ayyukan Gona da ke kan titin Kaduna zuwa Zariya cikin Jihar Kaduna ta shirya.
Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya samu wakilcin ministan ma’aikatar ciniki da zuba jari, Otumba Richard Adeniyi Adebayo ya bayyana cewa Gwamnatin tarayya a shirye take ta ci gaba da yin shirin hadin Gwiwa da bangarori masu zaman kansu da nufin bunkasa tattalin arzikin kasa.
Ministan ya ci gaba da cewa Gwamnati na kokarin ganin an inganta kowane bangare na harkokin kasuwanci da zuba jari don ganin tattalin arzikin kasa ya ci gaba da inganta.
Kamar yadda ya ce, “batun annobar cutar Korona da ta haifarwa da duniya samun matsalolin lalacewar farashi danyen mai,lalacewar kudin kasashen waje da zuba jari, hakan ya Sanya dole ayi tunanin wadansu hanyoyin daban na zuba jari domin samawa tattalin arzikin kasa hanyoyin tsaro.
Tun da farko Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i, wanda ya samu wakilcin Kwamishinan ma’aikatar kasuwanci, kirkire kirkire da kimiyya da fasaha, Farfesa Kabiru Mato, godewa Jagororin kasuwar duniyar ya yi kan irin yadda suke gudanar da kasuwar a kowace shekara, abin da ya bayyana da cewa zai taimakawa kamfanoni su rika samun baje kolin kayayyakinsu wanda hakan na kara bunkasa tattalin arzikin Jihar.
Mato ya ci gaba da bayanin cewa Gwamnati na yin ingantattun tsare tsaren da ke taimakawa wajen bunkasa al’amuran ciyar da matasa gaba.
A nasu bangaren wadanda suka shirya kasuwar karo na 43 sun tabbatarwa mahalarta kasuwar samun ingantaccen tsarin tsaro a baki dayan lokacin da za a gudanar da taron cin kasuwar.
Shugaban Kwamitin tsaro Jibril Hassan “sarkin yaki” ya bayar da tabbacin samun tsaro mai inganci kwarai, kasancewar yadda aka yi tanaji mai inganci.
“An yi kyakkyawan shirin tabbatar da samun ingantaccen tsaro a kasuwar da suka hada da samar da jami’an yan Sanda, Sojoji,jami’an tsaron DSS, KASTLEA, KADVIS da sauran masu aikin tsaron da kai duk baki daya.
“Ba zamu yi sako sako da batun tsaro ba wanda hakan ya sa muka samu kowane bangaren tsaro suna nan a kasuwar duniya domin taron dukiya da lafiyar jama’a da suka hada da masu kawo kayayyakinsu da masu halartar kasuwar domin kula duk wata hulda ta kasuwanci.
Hassan ya kara da cewa kafin a fara gudanar da wannan kasuwar sai da kwamitin tsaron da yake yi wa jagoranci ya ziyarci hukumar kwana kwana masu aikin kashe Gobara domin gujewa samun duk wata barazanar da ka iya tasowa.