Dokar Zabe: Buhari Ya Kunyata ‘Yan Adawa – Saliu Mustapha

0
420

Daga; MUSTAPHA IMRANA.

DAN takarar da ke kan gaba wajen neman kujerar shugaban Jam’iyyar APC na kasa Malam Saliu Mustapha, ya yaba wa shugaba Muhammadu Buhari da ya kunyata yan adawar siyasa da suke ta soki- burutsu a game da batun sanyawa dokar zabe ta 2022 hannu.

Saliu Mustapha ya bayyana hakan ne a cikin wata takarda da ke dauke da sa hannun mai taimaka masa a kan harkokin hulda da kafofin yada labarai, Dapo Okubanjo, inda ya bayyana a cikin takardar cewa a matsayinsa na mai goyawa shugaba Buhari baya, ya san hakika ba wanda ya kama kafarsa a wajen kokarin inganta al’amuran Dimokuradiyya.

“Shugaba Buhari na kan gaba wajen ganin Dimokuradiyya ta ci gaba da inganta, don haka babu shakku ko kadan wajen yarda da nagartarsa a kan dabbaka tsarin Dimokuradiyya wanda hakan ne ya sa ya nuna cewa ba wai jam’iyyu su tsaya a kan batun zaben fitar da dan takara na kai tsaye ba, don haka ya ce ayi wani tsarin zaben kuma duk a hada baki daya.

“Don haka tun da an samu wannan tsarin shima, don haka babu wata tantama shugaba Buhari zai yi kokarin tuntuba domin ganin kowane irin tsarin samar da sabuwar doka ya yi dai- dai da tanajin Dimokuradiyya kafin ya Sanya masa hannu ya zama doka.

“Ni na amince kamar yadda shugaba Buhari ya ce a cikin jawabinsa lokacin da yake Sanya wa dokar hannu, gyaran zai taimaka wajen samun komai ya inganta cikin tsari, tsari mai kyau da tabbatar da gaskiya da adalci a game da gudanar da zabe, da kuma rage batun matsalar samun takaddama da ka iya tasowa bayan zabe inda wasu ke kin amincewa ko kuma ma jam’iyyu baki daya su ki amincewa sam da zaben”.

“A game da shugabancin adawa kuma na jam’iyyar PDP da suke ta kokarin sanyawa wasu daga cikin yan Najeriya shakku a zukatansu game da lamarin zabe, ina fatan a yanzu da yadda shugaban kasa ya Sanya wa dokar hannu shikenan sai su yi shuru da bakinsu domin ba su da bakin magana”.

Turakin na Ilori ya kuma yi wa majalisun dokoki biyu godiya da suka aiwatar da kyakkyawan aiki domin ci gaban kasa, ya kuma yi kira a gare su da su yi aiki da shawarar shugaban kasa game da ayar doka mai lamba 84 na sabuwar dokar zabe.

Leave a Reply