Amnesty ta soki hukunci da aka yi wa su Mubarak Uniquepikin

0
268

Ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta Amnesty International ta yi Allah wadai da hukuncin da aka yanke wa matasan nan biyu masu amfani da shafin TikTok a jihar Kano saboda ɓata sunan gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Tun da farko dai matasan biyu masu suna Mubarak Muhammad alias wanda aka fi sani da Uniquepikin a shafin, da kuma Nazifi Muhammad, sun amsa laifinsu tare da neman sassauci daga kotu.

An kuma yanke musu hukuncin bulala 20 kowannensu da kuma biyan tarar 10,000 tare da share kotu na tsawon wata guda. Kungiyar ta Amnesty International ta ce kama yaran tare da tsare su a gidan yari kafin a yanke musu hukunci abu ne da ya saɓa wa doka, ta kuma yi kira da a saki yaran ba tare da wani sharadi ba.

KU KUMA KARANTA: <strong>Kotu ta yanke wa su Mubarak Pikin hukuncin bulala ashirin</strong>

Haka kuma ƙungiyar ta zargi alƙalin da cewa mai bin umarnin gwamnatin jihar ne. Tuni dai aka fara zartar da wasu daga cikin hukunce-hukunce, inda aka yi musu bulalar a gaban jama’ar da ke harabar kotun, sannan kuma sun biya tarar.

Lauyan matasan ya ce sun amince da hukuncin kotun, dan haka ba za su daukaka kara ba.

Leave a Reply