Amfani, da kuma illolin tsamiya a jikin Ɗan adam

Tsamiya na ɗaya daga cikin dangin ‘ya’yan itatuwan da al’ummar Hausawa musamman a Najeriya da kuma mutanen birnin Sin ke amfani da su sosai a rayuwar su ta yau da kullum. Ganin yadda ake yawan amfani da tsamiya a watan azumi, wajen yin kunu da kuma lemo, yasa Neptune Hausa ta binciko muku abubuwan daya kamata mu sani game da tsamiya.

Ta na ƙunshe da sunadarai kamar haka: Magnesium, Potassium, Iron, Calcium, Phosphorus, Vitamin B1 (thiamin), Vitamin B2 (riboflavin), Vitamin B3 (niacin), vitamin C, vitamin K, vitamin B6 (pyridoxine), folate, vitamin B5 (pantothenic acid), copper da kuma selenium.

Tsamiya tanada tasirai masu tarin yawa ta fuskar inganta lafiya, haka kuma tana wasu illoli idan aka sha ta ba bisa ƙa’ida ba. Ana amfani da tsamiya wajen sarrafa abubuwan sha, wajen yin magani, da kuma a girke-girke a matsayin abun ƙarin dandano.

Ga wasu jerin matsaloli da tsamiya ke magancewa a jikin bil Adama kamar haka:
1.Tsamiya na maganin cushewar ciki da rashin yin bahaya.

  1. Tana maganin mura da zazzaɓi.
  2. Tana maganin ciwon ciki.
  3. Tana maganin tashin zuciya ga masu ciki.
  4. Tana fitar da tsutsar ciki.

6.Tsamiya na magance Matsolin da suka shafi hanta da maɗaciya.

KU KUMA KARANTA: Amfanin Habbatatussauda ga ɗan adam

  1. Tana wanke dattin ciki da kuma cushewar hanji.
  2. Ana amfani da ganyen tsamiya wajen magance cutukkan daji (cancer)
  3. Ana tafasa ruwanta ayi wanka dashi don magance ciwon gaɓobin jiki.
  4. Tana sanya cin abinci domin kuwa tana sanya saurin jin yunwa.

Abubuwan kiyaye wa game da shan tsamiya

  1. Ga ramammu, yawan shan tsamiya na iya ƙara rama. Ga masu ƙiba kuwa, za ta taimaka masu wajen rage ƙiba.
  2. Ba a son a sha tsamiya da magungunan Ibuprofen da Aspirin saboda ta na ƙara adadin su da ke shiga jini. Idan haka ya faru, magungunan ka iya yin yawa su haifar da matsala.
  3. Shan tsamiya a kai a kai yana rage ƙarfin sha’awar namiji.

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *