Ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a jihohin Neja da Filato a Najeriya

0
554

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Hukumomi a jihar Filato sun ce gomman gidaje ne suka rushe sanadin ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar, lamarin da ya shafi ɗaruruwan magidanta.

Ruwan saman da aka samu kamar da bakin ƙwarya a ranar Laraba ne ya haddasa ambaliyar ta yi wannan gagarumar ɓarna. Ɗaya daga cikin waɗanda ambaliyar ta shafa a Jos babban birnin jihar Filato, yace awa huɗu aka kwashe ana tafka ruwan saman, kuma ya yi sanadin rushewar gomman gidaje da lalata dukiya. Mutumin ya ce yawancin waɗanda ambaliyar ta shafa, sun samu mafaka ne a gidajen ‘yan uwa da abokan arziki.

Muƙaddashin sakataren hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Fitalo, Mista Chuwang, ya ce gidaje sun ruguje, dukiya ta salwanta, ruwan ya yi awon gaba da kaya, mutane na cikin halin rashin tabbas da neman agaji.

A jihar Neja ma, hukumomi na can suna ƙoƙarin tantance barnar da ambaliyar ruwan sama ta yi musamman a yankin Kwantagora. Hukumomin jihar sun duƙufa don kididdige yawan asarar da aka samu sanadiyar ambaliyar ruwan a Kwantagora.

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa na jihar Ahmad Ibrahim Inga, yace za su ƙara tura tawaga ta musamman da kayan aiki don tallafawa mutanen da ambaliyar ta shafa.

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin cewa wasu jihohi za su fuskanci ruwan sama kamar da bakin kwarya na tsawon kwanaki huɗu daga ranar Laraba har zuwa Asabar.

Sannan tun kafin shi ɗin ma, anata kokawa da ƙaruwar ruwan saman da manazarta ke cewa a wasu lokutan ake shafe tsawon kwana ko wuni guda ana yi.

Leave a Reply