Wani mutum mai shekaru 37 ya kashe mahaifansa da muciya a Jigawa

0
340

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Wani matashi ɗan shekara 37 mai suna Munkaila Adamu ya kashe iyayensa a ƙaramar hukumar Gagarawa ta jihar Jigawa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Lawan Shiisu Adam wanda ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a Unguwar Malamai da ke garin Gagarawa, kamar yadda rahoton ya bayyana.

Shiisu ya bayyana cewa wanda ake zargin ya yi amfani da bindigar katako inda ya kaiwa mahaifinsa da mahaifiyarsa hari a dakinsu.

Ya ce ‘yan sanda sun yi nasarar cafke wanda ake zargin kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.

Kawo yanzu dai ba a san dalilin ɗaukar wannan matakin ba.

Leave a Reply