Ambaliyar ruwa ta kashe mutane tara, gidaje 6,417 sun lalace a Kano

Daga Saleh INUWA, Kano

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA) ta tabbatar da rushewar gidaje 6,417 da kadarori da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 541.6 da ambaliyar ruwa da iska ya lalata a ƙananan hukumomi 10 daga watan Afrilu zuwa yau.

Sale Jili, babban sakataren hukumar SEMA ne ya tabbatar da hakan jiya a Kano.

“Mutane tara ne suka mutu, gidaje 6,417 sun lalace, mutane tara suka jikkata, sannan anyi asarar dukiyoyin da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 541.6 sakamakon ambaliyar ruwa da iska a jihar,” Mista Jili ya ce.

Ambaliyar ta shafi ƙananan hukumomin Doguwa, Kibiya, ƙiru, Rano, Danbatta, Tsanyawa, Gwale, Ajingi, Dawakin Kudu da Albasu.

“Mun ziyarci Rano, Danbatta, Ajingi da Gwale domin raba kayan agaji ga wadanda abin ya shafa a matsayin matakan rage musu radadi,” inji shi.

Kayayyakin da aka raba wa waɗanda abin ya shafa sun haɗa da kayan abinci, buhunan siminti, kwanikan rufi, tabarmi, barguna, matashin kai da man girki, da sauransu, in ji jami’in.

Shugaban na SEMA ya kuma bayyana cewa hukumar ta tura jami’ai zuwa dukkan ƙananan hukumomi 10 da abin ya shafa domin gudanar da tantancewa, domin ta samu damar samar da cikakkun bayanai da kuma taimakawa waɗanda abin ya shafa.

Mista Jili ya yi kira ga jama’a da su kai rahoton duk wani bala’i ga shugaban hukumarsu, ya kuma gargadi mazauna yankin da su daina zubar da shara a magudanan ruwa tare da share magudanun ruwa domin gujewa ambaliya.

Jami’in hukumar agajin gaggawar ya ƙara da cewa “Mazauna a kusa da wuraren da ake fama da ambaliyar ruwa su tashi su kare rayukansu da dukiyoyinsu.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *