Jami’an ‘yan sanda sun cafke dattijuwa da ta sace yara 3 a Borno

0
294

Wata mata ‘yar Kimanin shekaru 60, mai suna Nsa Heneswa da ake zargi da safarar mutane ta shiga hannun ‘yan sanda a birnin Maiduguri na jihar Borno. An kamata ne tare da Almajirai biyu, da yarinya ‘yar shekara biyu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abdu Umar ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Maiduguri. Ya ce an kama wadda ake zargin ne a tashar mota ta Borno Express ranar 4 ga watan Agusta. Umar ya ce wadda ake zargin ta shiga Maiduguri ne a ranar 3 ga watan Agusta, inda ta je kai tsaye kasuwar Litinin inda ta ga wasu yara marasa galihu da aka fi sani da “Almajiri” suna bara a hanya.

A cewarsa, wadda ake zargin ta kira ɗaya daga cikin yaran ne ta ba shi Naira 200 sannan ta nemi ya raka ta domin ta saya masa kaya.

Daga nan sai ta koma cikin garin domin neman wani yaron,” inji shi. Umar ya ce wanda ake zargin ta isa unguwar Yan’ Nono da ke unguwar Bulumkutu inda ta yi awon gaba da wani yaro na Misis Amina Ayuba, wata mai sana’ar sayar da nono.

“Lokacin da ta isa tashar mota, ta nemi motar da za ta je Legas amma ‘yan kungiyar sun shaida mata cewa tuni ta tashi. “Sai ta nemi wurin zama kafin gobe. “Sai ta ƙara fita ta ɗauki ɗa na uku, sai dubunta ya cika, sa’a ta ƙare mata lokacin da ta yanke shawarar kai ɗaya daga cikin yaran gidan cin abinci,” in ji shi.

CP ya ce wani direba ne da ke aiki a layin Abuja a tashar motocin yayi shakku kan matar, yadda yaga tana abu kamar mara gaskiya, inda ya sanar da jami’an tsaro da su sa ido da tsaro a tashar motar.

Ya ce an kama wadda ake zargin tare da miƙa ta ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike. Tana shirin kai yaran Legas. Umar ya ce mai yiwuwa wadda ake zargin tare da wadanda ke da hannu a cikinta sun daɗe suna sana’ar saye da sayar da yara kafin doka ta kama ta.

Da take magana da NAN a hannun ‘yan sanda, ta ce: “A gaskiya, wannan shine karo na farko da nake yin hakan. “Ban taɓa yin haka ba. Wata mata ce a Legas ta gabatar da ni ga wannan sana’a. “Ina kuma da wata ma’aikaciyar jinya da ke taimaka min a asibitin kwararru na Maiduguri,” in ji ta.

Leave a Reply