Ambaliyar ruwa na cigaba da lalata ƙauyuka tare da janyo asarar rayuka a yankin Hadejia

0
582

Daga Abubakar TAHIR, Hadejia

Ambaliyar ruwa wanda ta fara ta’azzara daga farkon watannan zuwa yanzu na cigaba da tashin ɗaruruwan ƙauyuka tare da laƙume rayukan al’umma, banda miliyoyin gonaki da suke cigaba salwanta.

Ya zuwa yanzu, ƙauyuka sama da ɗari ne wannan lamarin yake cigaba da shafa. Al’ummar ke neman tallafin hukumomin da ƙungiyoyin agajin gaggawa na duniya. Garuruwan kamar su Tage, Masama, Kubayau, Gudito, Jiyan Jiba, Tafa dss ne ruwan ya tasa a cikin kwanaki nan inda Al’ummar ke fama da halin kunci.

Ko a ranar Asabar ɗinnan da ta wuce, babbar gadar dake hada al’ummar jihohin Bauchi zuwa Jigawa wanda ake kira da gadar Kogin Dole ta fashe, wanda babu damar wucewa. Haka asabar da dare wani jirgin kwalekwale ya kife da mutane 23 kamar yadda jami’an hulɗa da jama’a na hukumar ‘yan sanda a Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam ya bayyanawa manema labarai.

Ya zuwa yanzu, jami’an yan sanda sun bayyana cewa mutane da ke rasa rayukansu a kullum daɗa ƙaruwar suke da adadi mai yawa. Al’ummar da ruwan ya raba da gidajen su na cigaba da gudun hijira zuwa firamare dake Hago, Wasu Makaranta Bello Bayi a Garin Hadejia da sauransu.

Saidai wani abun tausayi shine halin ko in kula daga nan ɓangare gwamnatin, ƙungiyoyin agajin gaggawa wanda al’umma suke roƙo a taimaka musu da abinci, da magani, da fatun buhu.Ya zuwa yanzu, ƙananan hukumomin Auyo, Kafin Hausa, Hadejia, Guri, KirikaSamma na cikin mawuyacin hali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here