Shugaban karamar hukumar Wase a jihar Filato, honourable Dakta Ado Buba, ya bayyana cewa gwamnatin sa zata siyo bindigogi domin raba wa kungiyoyin sa kai na karamar hukumar.
Buba ya ce zuwa yanzu ƙaramar hukumar ta siyo kuma ta raba wa kungiyoyin sa kai bindigogi ƙirar ‘pump action’ 80 a karamar hukumar.
“Ƙaramar hukumar na kokarin karo bindigogi domin kare rayuka da dukiyoyin mutane amma rashin kudi ya hana hakan.
“Gwamnatina ta siyo wadannan bindigogi ne ganin yadda rashi tsaro ya zama ruwan dare a karamar hukumar Wase.”
Ya ƙara da cewa, “dalilin rashin tsaro manoma da dama a ƙaramar hukumar sa sun kasa zuwa gona a shekarar bara, samar da bindigogi wa kungiyar ‘yan sa kan zai taimaka wajen ganin bana manoma sun koma gona.”