Wasu ƴan bindiga a Najeriya sun yi garkuwa da aƙalla mutum 87 da suka hada da mata da yara a jihar Kaduna, kamar yadda mazauna garin da ‘yan sanda suka bayyana a ranar Litinin.
Kakakin rundunar ƴan sandan Kaduna Mansur Hassan ya tabbatar da faruwar lamarin, wanda ya ce ya faru a ƙauyen Kajuru a daren Lahadi amma bai iya bayyana adadin waɗanda suka ɓata ba.
Wani hakimin ƙauyen, Tanko Wada Sarkin ya ce an sace mutum 87. “Ya zuwa yanzu mun sami labarin dawowar mutane biyar da suka koma gida da suka tsere ta cikin daji,” kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho.
Sace mutane da gungun masu aikata laifuka ke yi don neman a biya su kudin fansa ya zama ruwan dare kullum a Nijeriya, musamman a arewacin kasar, inda ake ganin hukumomi ba su da ikon hana su.
KU KUMA KARANTA: Ƴan bindigar da suka sace ɗalibai 286 sun buƙaci kuɗin fansa naira biliyan ɗaya
Wasu rahotannin sun ce ɓarayin sun kuma fasa shaguna da gidajen mutane suka yi sata.
Shi ma shugaban ƙaramar hukumar Kajuru Ibrahim Gajere ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa ƴan bindigan sun kutsa garin da misalin karfe tara na dare a ranar Lahadi.
Ya kuma koka kan yadda ake yawan satar mutane a Kajuru a baya-bayan nan, lamarin da ke sanya mutane cikin tsoro da fargaba sosai.
Ko a ranar 7 ga Maris, an sace daliban wata firamaren gwamnati 287 da hedimasta da wasu ma’aikata a karamar hukumar Kuriga a jihar Kaduna. Masu garkuwa da mutanen na neman kudin fansa domin su sako daliban a cewar hukumar makarantar.
Sai dai a ranar Asabar shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi gargadi game da biyan kudin fansa ga ‘yan fashi ko ‘yan ta’adda ko kuma masu dauke da makamai domin a sako mutanen da aka sace.