‘Yansanda a Jigawa sun kama ango da abokansa bayan mutuwar amarya
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Rundunar ‘yansanda ta jihar Jigawa ta cafke mutum huɗu, ciki har da wani ango, Auwal Abdulwahab, mai shekara 20, bisa zargin hannu a mutuwar amaryarsa a ƙaramar hukumar Sule Tankarkar.
Lamarin ya faru ne da daren Asabar, inda ake zargin ango tare da wasu abokansa uku — Nura Basiru, Muttaka Lawan, da Hamisu Musa, dukkansu mazauna ƙauyen Tungo — da tilasta wa amaryar yin jima’i da su.
A cewar rahotannin, amaryar ta rasu yayin ƙoƙarin tursasa mata hakan.
Bayan samun rahoton, jami’an ‘yan sanda suka garzaya wurin inda suka ɗauki gawar mamaciyar zuwa Asibitin Ƙwararru na Gumel.
KU KUMA KARANTA:An ɗaure ɗan shekara 17 shekaru 14 a kurkuku saboda fyaɗe
Likitan da ya duba ta ya tabbatar da rasuwarta, kuma daga bisani aka mika gawarta ga iyalanta domin gudanar da jana’iza.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jigawa ya bayyana cewa waɗanda ake zargi za su fuskanci tuhume-tuhume na haɗin baki da kisan kai.
Haka kuma, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP AT Abdullahi, ya bada umarnin a mika su zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da ke Dutse domin gudanar da cikakken bincike.









