Ƙarancin wutar lantarki a Kano ya sa al’umma suna ta rubibin sayan ƙanƙara

0
427
Ƙarancin wutar lantarki a Kano ya sa al'umma suna tq rubibin sayan ƙanƙara

Ƙarancin wutar lantarki a Kano ya sa al’umma suna ta rubibin sayan ƙanƙara

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Sakamakon karancin wutar lantarki a Jihar Kano, ya tilastawa wasu daga cikin mazauna jihar sayan kankara domin samun saukin matsanancin zafin da suke sha.

Jaridar Neptune Prime ta ziyarci kasuwar kankara ta Sharada phase 1, Aisha Isah guda daga cikin wadanda sukaje sayan kankara, tace kullum tana sayan kankara guda daya, kuma tana isarta tasha tundaga safe zuwa dare”

Wani Magidanci damuka zanta da shi shima yace “yazo sanya kankara domin idan bai samu ya sha abu mai sanyi ba yana shiga cikin damuwa, sakamakon matsanancin zafi”

KU KUMA KARANTA:Rashin wutar lantarki a Kano, ya jawo gagarumar asara a kamfanoni

Haka tasa “Neptune Prime ta zanta da Malam Musa mai sayar da kankara, yace rabon sa da ya samu ciniki irin na wannan lokaci tun azumin Ramadan, wanda bayan Azumi yana sayar da kankara Naira Dari Uku Da Hamsin 350, amma yanzu suna sayar da kankara akan Naira Dari Biyar 500, zuwa Naira Dari Shida 600,

“Yanzu haka yana iya cinki a kullum kamar Dubu Arba’in zuwa sama, wataran kankarar tana karewa da wuri, sai ya je yasamu a wajen makwabtansa”, a cewar Malam Musa mai sayar da kankara.

Dr Munzali Alkasim likitan kashi asibitin Murtala Muhammad da ke Kano “ya shawarci jama’a da su rage shan kankara, wanda ya ce shanta kan haifar da illa ga lafiyar Bil’adam, yace a runga shan ruwa wanda ya zama shi bamai sanyi ba Kuma bamai zafi ba, daga karshe ya shawarci iyaye mata da su rage fita cikin rana tare da yara, wanda shi kanshi babba shima bai kamata ya ringa fita ba, a lokacin da rana ta bude ba.

Leave a Reply