Rashin wutar lantarki a Kano, ya jawo gagarumar asara a kamfanoni
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Raguwar karancin wutar lantarki a Kano ya haifar da gagarumar asarar dukiya ga masu manyan kamfanoni, da kanana dama sauran daidaikun masu sana’ar da ya shafi wutar a Kano,
Kusan sati Uku kenan, jahohin da suka hadar da Kano, Jigawa, Katsina, suka fada cikin yanayin karancin hasken wutar lantarki.
Kano na daya daga cikin jahohin dake takama da harkokin kasuwanci, wanda manyan kamfanoni suke harkokinsu a ciki,
Sai dai zuwa yanzu rashin wutar na barazana ga masu huldar kasuwanci su a wannan Jiha, hakan yasa masu kamfanoni suka fara samun durkushewa, kamar yadda wasu daga cikin su suka bayyanawa Jaridar Neptune Prime.
KU KUMA KARANTA:Mum shafe kwanaki 40 babu wutar lantarki – Mazauna lokon Maƙera ta jihar Kano
Sunce sakamakon rashin samun wutar, sun yi asarar dumbun dukiyoyin su, zuwa yanzu wasu kamfanoni sai dai su sayi man diesel, wasu Petro, wasu kuma sun hakura da harkokin su na kasuwancin su.
Alhaji Musa Mustapha Musa, guda ne daga cikin masu manyan-manyan kamfanoni a Kano yace sun tuntubi bangaren masu kula da hasken wutar lantarki reshen Kano, sai dai an bayyana musu cewar kamfanin na gyaran injinoni sabida karatowar damina, sai dai ya yi kausassan suka a kan haka.
Inda yace “kamata ya yi tun lokacin sanyi ace anyi gyara, kawai da alama su ake akashe kasuwanci arewa sabida Kano itace cibiyar kasuwanci, idan ta sami damuwa to babu shakka arewa ta sami matsala”, a cewar sa.
Suma al’ummar dake rayuwa a Kano sunce rashin wutar na barazana ga lafiyar su, sakamakon matsanancin zafi da suke sha, sunyi kira ga Gwamnan Kano wajen tsayawa domin gannin an dawo da wutar a Jihar.